Home Back

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi ya tsallake karatu na ɗaya a majalisar dokokin Kano

dalafmkano.com 2024/6/16

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano, ya tsallake karatu na ɗaya a zauren majalisar dokokin jihar.

Ƙudurin ya kai wannan mataki ne yayin zaman majalisar na yau Laraba, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan da akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Ɗiso, ya gabatar da karatun na ɗaya.

Har ila yau, yayin zaman na yau, majalisar ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta tallafa wa wasu kanikawa da kafintoci bisa iftila’in gobarar da ta ƙone musu kaya na miliyoyin Naira, tare da asarar rayuka a kan titin Lawan Dambazau.

Majalisar ta buƙaci hakan ne biyo bayan ƙudurin gaggawa da wakilin ƙaramar hukumar Birni da kewaye Alhaji Sarki Aliyu Daneji ya gabatar.

Yayin gabatar da ƙuɗurin, ɗan majalisar ya nemi gwamnatin data tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa domin rage musu raɗaɗin iftila’in.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin da ta ɗaga darajar asibitin garin Gano, zuwa matakin babban asibiti domin ƙara inganta kiwon lafiya a yankin har ma da sauran yankuna, kamar yadda ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Shu’aibu Rabi’u ya buƙata.

Wakilinmu na majalisar Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, a dai zaman na yau Laraba, shi ma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙaraye, Injiniya Ahmed Ibrahim, ya gabatar da ƙudurin neman gwamnatin Kano ta gina titi a hanyar da ta tashi daga mahaɗar titin zuwa sansanin horas da matasa ƴan hidimar ƙasa, ta bi ta Kurugu da Dederi har zuwa Yammedi duk a yankin ƙaramar hukumar Ƙaraye.

People are also reading