Home Back

'Zai yi wuya a ƙara samun juyin mulki a Najeriya'

bbc.com 2024/7/3
...

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Azeezat Olaoluwa
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos

Najeriya, wadda a abaya ta yi ƙaurin suna wajen yawan juyin mulki, yanzu ta cika shekara 25 a kan tafarkin dimokuraɗiyya, a daidai lokacin da ƙasashen yammacin Afirka da yawa suka fuskanci juyin mulkin cikin shekarun baya-bayan nan.

An yi shagulgula da kaɗe-kaɗe a ranar Laraba yayin da dandazon mutane suka riƙa tafi a lokacin da shugaban ƙasa ya yi jawabi - to amma mutane da dama za su riƙa kokwanton ko akwai wani dalili na yin murnar kwashe wannan lokaci a kan tafarkin dimokuraɗiyya.

Yayin da al'ummar Najeriya da dama ke fama da matsin rayuwa sanadiyyar lalacewar tattalin arziƙi da tashin farashin kayan masarufi, wasu da dama na nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al'amuran gwamnati.

Wata ƙuri'ar jin ra'ayin al'umma da cibiyar Afrobarometer mai yin bincike kan ra'ayin al'umma a nahiyar Afirka ta gudanar a 2022, ta nuna cewa kashi uku cikin huɗu na al'ummar Najeriya da aka tattauna da su - ko dai ba su jin daɗin yadda ake tafiyar da mulkin dimokuraɗiyyar ƙasar baki ɗaya ko kuma ba su gamsu da yadda ake tafiyar da wasu al'amuran ƙasar ba.

Wannan ba labari ne mai daɗi ba ga Najeriyar, wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Sai dai duk da haka, binciken ya nuna cewa mafi yawan al'ummar Najeriya sun fi son mulkin dimokuraɗiyya a kan kowane irin mulki.

Wataƙila saboda har yanzu ba su manta da abubuwan da suka faru a lokacin mulkin sojoji ba.

Tun bayan samun ƴancin kai a 1960, gwamnatocin farar hula ba su daɗe suna mulki ba, inda sojoji suka ja ragamar ƙasar a mafi yawan shekarun da ta kwashe.

Wani masanin tarihi, Farfesa Kayode Soremekun ya ce: "Yanzu zai yi wahala a yi juyin mulki a Najeriya".

"Sojoji sun wuce zamaninsu. A tsawon lokaci an gano cewa su ma sojoji za su iya zamowa gurɓatattu tamkar ƴan siyasa. Shi ya sa yanzu mafi yawan ƴan Najeriya ba su kallon su a matsayin masu gaskiya," in ji shi.

Asalin hoton, AFP

The military band plays musical instruments during celebrations marking Democracy Day in Abuja, on June 12, 2019
Bayanan hoto, Sojoji masu badujala sun halarci bikin cikar dimokuradiyyar Najeriya shekara 25

Wani dattijo mai shekara 59 a duniya, Adedeji Adekunle ya shaida wa BBC cewa mulkin soja cike yake da danniya da zalunci.

Mutumin, wanda a yanzu yake sana'ar tsara bubukuwa ya tuno wani abu da ya faru da shi a farkon shekarar 1998, lokacin yana ɗalibi.

Ya ce "A shekarun baya na shiga zanga-zangar koran sojoji ta 'military-must-go' a Legas inda sojoji suka kai mana farmaki suka kama mu. An azabtar da da dama daga cikin mu, yanayi ne mai tayar da hankali."

Ƙungiyar kare hakkin bila'adama ta Human Rights Watch ta ce lokacin mulkin soji na shekarun 1980 zuwa 1990 ya kasance lokaci ne na lalacewar tattalin arziƙi da take hakkin bil'adama.

Bayan rasuwar shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Sani Abacha a 1998, wanda ya gaje shi, Janar Abdulsalami Abubakar ya yi alƙawarin gudanar da zaɓe tare da mayar da ƙasar kan tafarkin dimokuraɗiyya bayan shekara ɗaya.

Tsohon ɗan majalisar dattijan Najeriya, Sanata Shehu Sani ya ce "komawar Najeriya kan tafarkin dimokuraɗiyya a 1999 ya sa mutane sun fara tunanen samun kyakkywar makoma a ƙasar, da ƴanci da tsaro da haɗin kai da kuma samun kwanciyar hankali".

Mista Adekunle ya gode wa Allah a lokacin da ƙasar ta koma mulkin dimokuraɗiyya.

Ya ce "Da dama daga cikinmu mun yi shakku kan cewa Janar Abdulsalami da gaske yake yi zai miƙa mulki ga farar hula, to amma a lokacin da aka yi zaɓe tare da sanar da wanda ya yi nasara, abubuwa sun sauya. Sai ya zamo tamkar ƙasar ta shiga wani sabon zamani."

To amma ga matasa waɗanda ba su san abubuwan da suka faru ba, ko ma ba a haife su ba a wancan lokacin, labarin abubuwan da suka faru a lokacin mulkin soji ba wani abu ba ne mai muhimmanci a gare su.

Asalin hoton, Getty Images

Nigeria's President Bola Tinubu (C) makes gesture during his inauguration at a swearing-in ceremony at the Eagle Square in Abuja, Nigeria on May 29, 2023
Bayanan hoto, A ranar da aka rantsar da shi Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur

Shugaban Najeriya mai ci, Bola Tinubu wanda ya kwashe shekara ɗaya kan mulki na fuskantar ƙalubalen yadda zai samu goyon bayan matasa ƴan Najeriya yayin da ake tsaka da matsanancin tattalin arziƙi, waɗanda wasu daga cikinsu shi ne ya kawo.

Matakin da ya ɗauka na cire tallafin man fetur da barin naira ta tantance darajarta a kasuwa sun haifar da tashin farashin kayan masarufi.

Ya ce an ɗauki waɗannan matakai ne domin daidaita tattalin arziƙi da ci gaban ƙasa a tsawon lokaci, amma waɗanda abin ya fi shafa na ganin cewa wannan ba mafita ba ce.

Sannan idan aka dubi shekara 25 da aka kwashe, duk da cewa kuɗin shiga na mai matsakaicin ƙarfi ya nunka sau huɗu, ga mutane da dama wannan bai yi wani amfani ba.

Gare su, abu mafi muhimmanci shi ne halin da ake ciki a yanzu.

A sanadiyyar haka, wasu matasa a Najeriya kamar MI Thomas, marubucin waƙoƙi mai shekara 33 a duniya, bai damu ba idan aka koma mulkin soja.

Ya ce: "Tun da na kai shekara 18 nake yin zaɓe amma duk shugabannin da na zaɓa sun ba ni kunya. Sojoji ba su wasa a mulkinsu. Suna ɗaukan matakai masu tsauri babu ɓata lokaci a harkar mulki."

Haka nan ma matasa da dama sun bayyana irin wannan ra'ayi a shafukan sada zumunta.

Abin da ke haifar da ƙaruwar irin wannan ra'ayi bai wuce rashin amana irin na ƴan siyasa ba saboda ƙin cika alƙawurra.

To amma kuma ƙila hangen-dala ne kawai a ɓangaren matasan, inda wasu ke cewa a lokacin mulkin soja babu rashin tsaro da rashawa kamar yadda ake da su yanzu.

Wasu labarai game da Najeriya:

Sai dai da alama wasu sun manta, misali, an ruwaito cewa tsohon shugaban ƙasar mulkin soja, Janar Sani Abacha ya kwashe tare da jibge kuɗin gwamnati masu maƙudan yawa a ƙasashen ƙetare.

An mayar wa Najeriya irin waɗannan kuɗaɗe da yawansu ya kai aƙalla dalar Amurka biliyan shida.

Kamar yadda aka yi tsammani, shugaba Tinubu bai cika son yin magana kan mulkin soji ba, musamman ganin cewa shi kansa an taɓa kulle shi sanadiyyar ayyukansa na goyon bayan dimokuraɗiyyya.

Jim kaɗan bayan hawa kan mulki, Tinubu ya ci karo da ƙalubalen warware rikicin juyin mulkin da aka samu a Jamhuriyar Nijar mai maƙwaftaka, inda ya ti alla-wadai da lamarin tare da barazanar ɗaukan mataki na soji - sai dai daga baya barazanar tasa ba ta haifar da komai ba.

A cikin gida kuwa, a nata ɓahgaren, rundunar sojin Najeriya ta ce ba ta da aniyar komawa cikin harkokin mulki.

A watan Fabarairu, babban hafsan hafsoshin Najeriya Christopher Musa ya ce: "mutanen da ke soki-burutsun cewa sojoji su ƙwace mulki ba masu son Najeriya ba ne".

"Muna sanar da mutane cewa sojojin Najeriya aikinsu kawai shi ne su kare dimokuraɗiyya. Dukkanmu muna son dimokuraɗiyya, abubuwa sun fi tafiya daidai l;okacin mulkin dimokuraɗiyya, saboda haka sojoji za su ci gaba da taimaka wa dimokuraɗiyya."

Asalin hoton, AFP

Picture dated 30 August shows Nigerian President General Sani Abacha at the last session of the summit meeting of the Economic Community of West African States (ECOWAS) in Abuja
Bayanan hoto, Tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Janar Sani Abacha

Cikin shekara 25 da aka kwashe - akwai lokutan da aka samu giɓi ta yadda sojoji za su iya yunƙurin karɓe mulki a Najeriya idan sun so, amma ba su yi yunƙurin hakan ba - kamar lokacin da aka rasa inda Shugaba Umaru Musa Ƴar'aduwa ya shiga saboda rashin lafiya.

Ɗan majalisar dokokin tarayya a Najeriya daga jihar Jigawa, Sanata Babangi Hussaini ya ce hakan ta faru ne saboda wasu matakai da aka ɗauka waɗanda suka "rage wa sojoji kwaɗayin ƙwace mulki tare kuma da ƙarfafa abubuwan da suka tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya".

Sanatan ya ce: "zai iya yiwuwa ba mu yi ƙoƙari kamar yadda ƴan Najeriya suka sa rai ba... amma dai an samu ci gaba".

Akwai kuma wasu masana, kamar farfesa Fidelis Allen waɗanda ke nuna rashin amincewa da cewar rashin katsalandan ɗin sojoji na nufin an samu ingantacciyar dimokuraɗiyya.

Tun daga shekara ta 1999 ne al'ummar Najeriya ke zaɓen shugabanni to amma akwai tantama kan yadda shugabannin ke kashe kuɗin gwamnati ba tare da iya bayar da cikakken bayani a kansu ba.

Farfesa Soremekun na ganin cewa har yanzu akwai jan aiki a gaba idan ana son dimokuraɗiyyar Najeriya ta zama mai inganci.

"Abu ne mai kyau, amma wajibi ne mutane su ci gajiyarta," in ji shi.

Amma ga mutane kamar Mista Adekunle wanda har yanzu ke tuna abubuwan da suka faru a lokacin mulkin sojoji, babu wani zaɓin da ya fi wannan.

"Dimokuraɗiyya na da daɗi, tana samar da ƴanci. Babu wani alfanu a cikin mulkin sojoji.

Tare da gudumawar Yusuf Akinpelu da Gift Ufuoma

People are also reading