Home Back

Kitson Sallah

leadership.ng 2024/7/2
Kitson Sallah

Kitso na daya daga cikin ababen da suke kara fidda tsarin kwalliyar Mace musamman in an sami kwararriyar mai kitso, kitso ya kasu kashi daban-daban akwai kitson hannu, da na Wibin wanda kowacan Mata idan aka ce Sallah ta gabato sukan yi kokarin ganin sun yi kitso na musamman ko kuma su yiwa yaransu, wanda zai birge kowa.

Yayin da wasu kuma suke yin shamfo, ko sangas, ko daure-daure da dai sauransu. Sai dai kuma wasu sukan rasa irin tsarin kitson da zai yi dai-dai da ra’ayinsu, morewa idanuwanki domin zaben kitson da ya fi dacewa da ke.

Lalle

Kunshi na daya daga cikin abubuwan da mata ke yi da zarar Sallah ta gabato, domin fidda tsarin kwalliya me kyau ya yin shagalin bikin Sallah.

Dinki

A kowacce sallah mata da maza na kokarin ganin sun fidda dinki na musamman wanda zai burge kowa, wani sa’in ma har akan fidda wani dinkin a saka masa suna wanda zai zama ya yi a wannan lokaci.

People are also reading