Home Back

Arsenal za ta koma son Luiz, Tsadar Branthwaite ta sa Man Utd ta karkata ga Todibo

bbc.com 2024/5/2
Douglas Luiz

Asalin hoton, Getty Images

Ana sa ran Arsenal ta sake nuna sha'awarta a kan dan wasan tsakiya na Aston Villa Douglas Luiz, na Brazil a bazaran nan. (Football Insider)

Fulham za ta yi zawarcin Trevoh Chalobah, na Chelsea domin maye gurbin dan bayanta Tosin Adarabioyo, wanda ake sa ran ya bar kungiyar a karshen kaka saboda kwantiraginsa ya kare. (Teamtalk)

Manchester United ta mayar da hankalinta kan dan bayan Nice Jean-Clair Todibo, dan Faransa mai shekara 24, saboda farashin da Everton ta sanya wa matashin dan bayanta Jarrad Branthwaite na Ingila mai shekara 21 ya yi mata yawa. (Teamtalk)

Jadon Sancho, zai iya sake komawa taka leda a Manchester United, daga zaman aro da yake a Borussia Dortmund, idan Erik ten Hag ya bar United. (i news)

Sannan kuma United din tana son sayar da Antony, dan Brazil a bazaran nan. (Rudy Galetti)

Bayer Leverkusen ta yi wa matashin dan wasanta na tsakiya Florian Wirtz na Jamus mai shekara 20, farashin yuro miliyan 150, yayin da Barcelona da Real Madrid ke nuna sha'awarsu a kansa. (Radio Marca daga Mundo Deportivo )

Arsenal da Liverpool na sha'awar dan bayan Eintracht Frankfurt Willian Pacho na Ecuador, mai shekara 22. (Florian Plettenberg)

Arsenal za ta sanya Eddie Nketiah, a kasuwa a bazaran nan, amma a farashin fam miliyan 40. (HITC)

Tottenham na nazarin zawarcin dan wasan tsakiya na Shakhtar Donetsk Giorgi Sudakov, na Ukraine mai shekara 21. (Caught Offside)

Newcastle ta sake nuna sha'awarta ta sayen dan wasan tsakiya na Nottingham Forest Morgan Gibbs-White, na Ingila 24. (Football Insider)

Liverpool na shirin nada David Woodfine a matsayin mataimakin darektan wasanni ga Richard Hughes, yayin da ya sake komawa Anfield kasa da shekara daya bayan ya bar kungiyar. (Liverpool Echo)

Manchester United za ta fara tattaunawa da matashin dan wasan tsakiya Kobbie Mainoo mai shekara 18, dan Ingila a kan sabon kwantiragi a bazaran nan. (Sun)

Everton na son tsawaita kwantiragin Dominic Calvert-Lewin, na Ingila, wanda kwantiraginsa na yanzu zai kare a karshen kaka mai zuwa. (Football Insider)

Wrexham na son sayen mai tsaron ragarta Arthur Okonkwo mai shekara 22, wanda Arsenal ta ba ta aro. (The Athletic)

Juventus za ta saurari tayi a kan dan wasanta na gaba na Italiya Federico Chiesa, wanda ake alakantawa da Liverpool da Newcastle, bayan sabanin da ya shiga tsakaninsa da kociyansu Massimiliano Allegri a kan inda zai rika wasa. (Tuttosport)

People are also reading