Home Back

RAGE FARASHIN GAS DAGA N1,650 ZUWA N1,000: Tinubu ya ce gaskiya Ɗangote namijin duniya ne

premiumtimesng.com 2024/5/11
RUWAN DARE GAME DUNIYA: Ɗangote zai raba shinkafar Naira biliyan 13 ga marasa galihu a jihohi 36

Shugaba Bola Tinubu ya jinjina wa Aliko Ɗangote da kamfanin sa na Ɗangote Oil and Gas Limited, bisa gagarimin ragin farashin gas da ya yi, wato dizal.

Shekaranjiya ne kamfanin Ɗangote ya zaftare farashin litar gas daga Naira 1,650 zuwa Naira 1,000 ga duk mai sayen lita miliyan 1 abin da ya yi sama.

An kuma yi ragin kashi 30 bisa 100 na farashin ga masu sayen lita miliyan 5 abin da ya yi sama a lokaci guda.

Wannan gagarumin ragi da Ɗangote ya yi, har na kashi 60 bisa 100, zai zama alherin da zai shafi kisan kowa, domin ragin zai saukar da tsadar farashin kayayyaki da dama a cikin Najeriya.

A kan haka ne Shugaba Tinubu ya jinjina ga Ɗangote da kamfanin, a kan hoɓɓasan rage farashin wanda ya ce zai haifar da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa, kuma zai inganta rayuwar al’umma.

Daga nan Tinubu ya yi kira ga hamshaƙan ‘yan kasuwa a Najeriya su riƙa cusa kishin ƙasa a kasuwannin su.

Ya tabbatar da cewa Najeriya a yanzu ƙasa ce wadda ke da damammakin da masu zuba jari za su yi harkokin kasuwancin su mai albarka sosai.

People are also reading