Home Back

BUNKASA ILIMI: Mata za su rika karatu tun daga Firamare har Jami’a kyauta ne a Jigawa – Gwamna Namadi

premiumtimesng.com 2024/6/28
Gwamnatin Kano ta sanar da wurare 12 da’yan makarantun kwana zasu rubuta jarabawa a ciki

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya raba rigunan makaranta ga dalibai mata dake makarantun sakandare a fadin Jihar.

Taron wanda ma’aikatar ilimin mai zurfi ta shirya ya fara rabon ne daga makarantar sakandaren mata na ‘Girls Science Secondary School’ dake Jahun a karamar hukumar Jahun.

Namadi ya ce gwamnatin sa za ta mai da hankali wajen saka yara mata a makarantun boko a jihar.

Ya ce a dalilin haka ya ce kowace ‘ya mace daga makarantar firamare zuwa Jami’a za ta yi karatu kyauta a jihar.

Gwamnan wanda ya jadadda cewa ilimin boko shine hanyar samun ci gaba ga kowace al’umma ya ce zai yi kokarin samar da ilimin boko ga kowa da kowa cikin sauki.

Namadi ya ce gwamnatin sa za ta samar da hanyoyin da malamai za su inganta kansu ta hanyar samun horon da ya kamata domin kara kwarewa a aikin su.

Bayan haka kwamishinan ilimin mai zurfi na jihar Isa Yusuf ya yaba kokarin da gwamnan ke yi wajen ganin mata sun shiga makarantan Boko a jihar.

Yusuf ya ce gwamnan Namadi zai gyara makarantun sakandare na mata 12 tare da raba takardu ga kowacce makaranta.

Ya ce gwamnan ya siyo kekunan dinki da sauran kaya domin horas da matan sana’o’in hannu wanda hakan ya ke cewa zai taimaka wajen karkato da hankulansu zuwa makaranta da ganin cewa sun kammala karatunsu.

Shugaban kungiyar shugabanin makarantun sakandare na jihar ANCOPSS Hajiya Asmau Sulaiman bayan ta mika godiyarta ga gwamnati ta ce aiyukkan da gwamnan ya yi zai taimaka wajen ganin kowace ‘ya mace ta samu ilimin boko a Jigawa.

People are also reading