Home Back

MARƘABU A KOTU: ‘Yadda aka damfari oga na fam miliyan 1 da nufin yi masa zafafan addu’o’in kankare masa zunubai’ – Direban oga

premiumtimesng.com 2024/4/29
court
court

Hukumar EFCC Reshen Shiyyar Legas, ta gabatar da mai bada shaida a gaban kotu, kan tuhumar da ake wa waɗansu da zargin damfarar zunzurutun kuɗi har fam miliyan 1.

Waɗanda ake tuhumar sun haɗa da Morufu Adewale, Omitogun Ajayi, Ajesegiri Abiodun, Abayomi Alaka, Taiwo Ahmed, Raufu Raheem da Sanlabiu Teslim.

An gurfanar da su a gaban Mai Shari’a R. A Oshodi na Kotun Ƙararrakin Musamman da ke Ikeja, Legas, a ranar 18 ga Maris.

An dai sake gurfanar da su ne a gaban Mai Shari’a Oshodi tun a cikin Disamba, 2022, bisa tuhumar su da laifi uku, bayan ɗauke shari’ar ta su daga hannun Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo, wanda a can ne aka fara gurfanar da su tun a ranar 3 ga Fabrairu, 2022.

An tuhumar su da haɗa baki a cikin watan Mayu da Yuli, 2018, sun karɓi fam na Ingila har miliyan 1 daga Dakta Lateef Oladimeji Bello, domin a yi masa zafafan addu’o’in kankare masa zunubai ita da iyalin sa baki ɗaya.

An ƙulla wannan yarjejeniya ce da niyyar cewa za a maida masa kuɗaɗen a cikin sati ɗaya, bayan kammala addu’ar.

Sai kuma tuhumar karɓar Naira miliyan 175,000,000 da nufin yi wa ɗan mutumin da sauran iyalin sa zafafan addu’o’in kankare zunubai.

Dukkan su dai sun ce ba su aikata laifin da ake tuhumar su ba. Daga nan aka fara shari’a.

A ranar Litinin, an gabatar da mai bada shaida, mai suna Moruf Quadri, wanda shi ne direban wanda aka damfara ɗin, kuma ya shaida wa kotu cewa tsawon shekaru 25 kenan shi ne direban ogan.

Ya bayyana wa kotu yadda ya riƙa ɗaukar ogan sa su na shiga cikin dazuka, ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba, ana yi masa “karkarar zunubi”.

Ya kuma shaida wa kotun yadda ‘yan damfarar suka riƙa karɓar kuɗaɗe wajen ogan sa, nau’in nairori da kuɗaɗen waje.

Lauya mai gabatar da mai bada shaida, N.K Ukoha ne ya gabatar da direban mutumin da aka damfara ɗin, kuma direban ya nuna dukkan waɗanda ake tuhumar, tare da bayyana wa kotun sunayen inkiya ɗin da suka raɗa wa kan su.

“Cikin watan Mayu, 2018, ni da Baba Sanlabiu da oga na mun je Ikenne, lokacin da muka isa, ya sauko shi da ɗan sa, suka shiga wani gida. Ni kuma na zauna cikin mota ban fita ba, suka shafe tsawon sa’o’i biyu a cikin gidan”, inji direban.

Ya kuma shaida wa kotun cewa ya riƙa tuƙa ogan sa su da wasu ‘yan damfarar da nuna a cikin kotun, su na shiga cikin surƙuƙin dajin Ijebu-Igbo da ke Jihar Ogun, sai kuma dajin Igbogbo da ke cikin Ikorodu, Jihar Legas.

Ya ce sau da yawa sha kai ogan sa a can dazukan, wanda sai babbar mota samfurin Jeep ce ke iya shiga cikin dajin.

“Sai da muka shafe sa’o’i takwas kafin mu shiga cikin dajin Ijebu-Igbo. A ciki kuma mun shafe sa’o’i uku su na ciki su na yin abin da suke yi, Ni kuma ina jiran su, kafin su fito.

“Sau da yawa kuma mukan tsaya wurin wani Bahaushe ɗan canji, a Legas, domin mu tura wa Ifakunle kuɗi.”

Ya ce kuɗaɗen da aka ba shi ya ɗauka ya bai wa Ifekunle sun kai cikin jakar Ghana Must Go 25.

Ya ce wasu lokutan ma ‘yan damfarar na sa su sayi raguna su kai masu.

Ya ce har sai da ta kai an sa sun tanadi wani gingimemen akwati, wanda ake tara masu kuɗaɗen a ciki.

Ya ce kuma an taɓa aika shi ya tura masu kuɗi ta asusun ajiyar bankin Eco Bank kamar sau biyu.

Ya shaida wa kotu cewa ‘yan damfarar sai da suka tsiyata ogar sa ƙarƙaf, har ta kai ko motar hawa ba ta da ita. Wadda ta ke hawan ta lalace, ta kasa gyarawa, ballantana a ce ta sai wata sabuwa.

Sai da ta kai da tsohuwar motar da na karɓi bashi daga hannun oga na na riƙa ɗaukar sa ina kai shi inda zai kai kuɗi.

“Har dai wata rana kan hanyar dawowar mu, muka afka wani rami motar ta yi tsayi, gwajab, daga nan ya dawo hayyacin sa, sai na ji ya ce “ha, an fa damfare Ni!”

Ya ce ogan sa ya garzaya cikin wani gida da aka ce ya rika tara kuɗaɗe cikin akwati, amma da ya ce bai samu ko sisi ba. Gidan a Ijebu-Igbo yake.

An dai ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 19 ga Maris, 2024.

 
People are also reading