Home Back

NCAA Ta Dakatar Da Wasu Jirage 10 Kan Rashin Sabunta Lasisi

leadership.ng 2024/8/25
NCAA Ta Dakatar Da Wasu Jirage 10 Kan Rashin Sabunta Lasisi

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Nijeriya NCAA, ta sanar da dakatar da wasu kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu 10, a sakamakon rashin sabunta takardun lasisin su.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, mai dauke da sa hannun daraktan hulda da jama’a na hukumar, Michael Achimugu, ya ce hukumar ta bayyana ta umurci duk masu lasisin yin hada-hadar zirga-zirgar jiragen sama su sake sabunta lasisin kafin ranar Afrilu 19, 2024.

NCAA ta ce: “Sakamakon rashin mutunta wannan doka, tun da farko NCAA ta dakatar da izinin gudanar da aiyukansu”.

Daga cikin kamfanunnukan jiragen da abun ya shafa sun hada da Azikel Dredging Nigeria Ltd da Bli-Aviation da Ferry Aviation Developments Ltd da Matrix Energy Ltd da Marrietta Management Services Ltd da Skypaths da Mattini Airline Services Ltd da Aero Lead Ltd da Sky Bird Air Ltd da kuma Ezuma Jets Ltd.

People are also reading