Gobara Ta Kama a Matatar Man Dangote, Kamfanin Ya Yi Martani Kan Lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - An shiga tashin hankali bayan wani bangare na matatar man Aliko Dangote ya kama da wuta.
Lamarin ya faru ne a yau Laraba 26 ga watan Yunin 2024 a sashen tsaftace ruwa na matatar da ake kira ETF.
Kakakin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina shi ya tabbatar da haka a shafin X a yau Labara 26 ga watan Yunin 2024.
Chiejina ya ce wutar ta kama ne a bangaren ETF da ke tace girbataccen ruwa a matatar da ke jihar Lagos.
Ya tabbatar da cewa an shawo kan matsalar inda ya ce ba wata babbar matsala ba ce kuma babu asara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun yi nasarar shawo kan matsalar wutar da yake ba babba ba ce a yau Laraba 26 ga watan Yunin 2024 a sashen ETF."
"Ba wani abin damuwa ba ne tun da matatar na ci gaba da aiki kuma babu rauni ko mutuwa daga bangaren ma'aikatanmu."
- Anthony Chiejina
Karin bayani na tafe...
Asali: Legit.ng