Home Back

Abin Tausayi: Mata Da Miji Sun Rasu A Yayin Aikin Hajjin Bana

leadership.ng 6 days ago
Abin Tausayi: Mata Da Miji Sun Rasu A Yayin Aikin Hajjin Bana

Wasu ma’auratan Jihar Maryland Alieu Dausy Wurie mai shekaru 71 da kuma Isatu Tejan Wurie mai shekaru 65 a duniya sun rasu sakamakon tsananin zafi lokacin aikin Hajji a ƙasar Saudiyya. A ranar 15 ga Yuni, an hango ma’auratan suna jiran jigilar kaya zuwa Dutsen Arafat a cikin zafin kashi 109©

Sun daɗe suna a taru da shirin yin wannan ibada, amma ashe zai zamo ƙarshen rayuwarsu, a cewar ɗiyarsu mai suna Saida Wurie.

An bayyana musabbabin mutuwar ma’auratan a matsayin tsananin zafin yanayi da zazzabi, kuma an binne su a Saudiyya kafin iyalansu su isa.

Saida Wurie ta bayyana jimamin yadda lamarin ya gudana, inda ta yi imanin cewa hukumar shirya tafiye-tafiye da suka bi ba ta shirya wa iyayenta yadda ya kamata ba don yin aikin hajji.

Wuries sun kashe dala 23,000 a tafiyar, suna yin rajista ta wani kamfani mai rijista na Maryland. Gani na ƙarshe da aka yi mu su shi ne sun yanke shawarar tafiya bayan sun daɗe suna jiran abin hawa.

Lamarin dai na daga cikin babban abin tausayi a lokacin aikin Hajjin bana, inda sama da mutane 1,300 suka mutu sakamakon tsananin zafi, inda yanayin zafi ya kai ma’aunin Fahrenheit 120.

Gwamnatin Masar na tuhumar jami’an shirya tafiye-tafiye kan “Damfara” a aikin Hajji bayan waɗannan mace-mace, inda kamfanonin yawon buɗe ido goma sha shida ke shirin rasa lasisin su.

People are also reading