Home Back

Boko Haram da Iyalen su 69 sun mika wuya ga sojojin a haɗin guiwa na MNJTF a Kamaru

premiumtimesng.com 2024/8/22
ZULUM YA FUSATA: “Wadanda suka ga komawa daji tare da Boko Haram ya fi musu, Allah ya kiyaye hanya”

Akalla Boko Haram da iyalen su 69 ne suka mika wuya ga sojojin hadaddiyar kungiyar ‘Multinational Joint Task Force’ a kasashen Kamaru da Niger.

Wannan sanarwa na kunshe a takardar da kakakin rundunar Abubakar Abdullahi ya aika daga Ndjamena dake Chadi zuwa Maiduguri jihar Borno a Najeriya ranar Talata.

“Boko Haram tare da iyalen su 69 sun mika wuya ga jami’an tsaro daga ranar daya zuwa shida ga Yuli bayan harin da sojojin Kamaru da Najeriya suka kai wa maharan a maboyar su.

Abdullahi ya ce daga cikin maharan da dakarun suka kama akwai maza 13, mata 43 sannan da yara kanana.

“A wannan lokaci wasu iyalen ‘yan ta’adda mutum 12 da a ciki akwai mata 5 da yara kanana 7 sun mika wuya ga hannun jami’an tsaron.

“Dakarun sun damka wadannan ‘yan ta’addan tare da iyalen su ga jami’an tsaron dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ dake Gamboru da Banki domin daukan mataki a kansu.

Bayan haka Abdullahi ya ce dakarun a ranar 1 ga Yuli sun kama wani dan ta’adda mai shekara 24 mai suna Tijjani Muhammad bayan ya mika wuya ga sojoji a Jamhuriyar Niger.

Ya ce dakarun sun kama dan ta’addan da bindiga kirar AK-47 da harsasai da dama.

“Muhammad ya shiga hannun jami’an tsaron ne bayan ya gudo daga sansanin Boko Haram dake Libiye Soroa saboda yawan harin da dakarun rundunar ‘Operation Lake Sanity II’ ke kai musu.

Abdullahi ya ce karfin gwiwar kai wa mutane hari da ‘yan ta’addan ke da shi ya ragu saboda yadda ‘yan ta’addan ke mika wuya hannun jami’an tsaro.

Kakakin ya yi kira ga ‘yan ta’addan da su ajiye makamai domin a samu zaman lafiya a kasar nan.

People are also reading