Abdullahi Ganduje: Kotu ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Shugabancin Jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje zai san matsayarsa kan jagorancin jam'iyyar yayin da kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari'ar.
Wasu 'yan jam'iyyar, karkashin inuwar 'yan APC na Arewa ta Tsakiya ne su ka shigar da kara bisa zargin cewa an kakaba masu Ganduje a matsayin shugaba.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayyana cewa wannan dambarwa za ta zo karshe ranar 18 Satumba, 2024 da za a yanke hukunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yau Juma'a ne Mai Shari'a Inyang Ekwo ya saurari lauyoyin Abdullahi Umar Ganduje da na 'yan jam'iyyar daga Arewa ta Tsakiya kan kalubalantar yadda ake shugabancin APC.
Wadanda su ka shigar da kara karkashin Saleh Zazzage na kalubalantar kasancewar Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam'iyyar APC bisa rashin cancanta, The Guardian ta wallafa.
Su na rokon kotun ta gaggauta haramtawa Abdullahi Umar Ganduje ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban APC kasancewar lokaci ne na dan jam'iyyar daga Arewa ta Tsakiya ya jagorancesu.
A wani labarin kun ji cewa tsohon dan takarar shugabancin jam'iyyar APC, Mohammed Sa'idu Etsu ya nemi kotu ta kori Abdullahi Ganduje daga kujerarsa.
Tsohon dan takarar ya nemi kotu ta kori Ganduje bisa zargin cewa a nada shi ba bisa ka'ida ba, wanda hakan ya saba da kundin tsarin mulkin jam'iyyar.
Asali: Legit.ng