NOA: Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Sanarwa Game da Sabon Taken Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Hukuma mai wayar da kan 'yan kasa (NOA) ta fitar da sabuwar sanarwa kan gyare-gyaren da ta ke a kan taken Najeriya.
Hukumar ta ce a halin yanzu tana tattaunawa ne da masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen da za a yiwa sabon taken.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa mataimakin daraktan yada labarai na hukumar ne ya sanar da haka a yau Talata a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta ce bayan canza taken an samu wanda suka rika yada wanda ba a tace ba a kafafen sadarwa.
Saboda haka ta sanar da cewa za ta fitar taken da aka tace nan ba da jimawa ba domin kaucewa amfani da wanda bai dace ba.
Hukumar NOA ta ce ta samu bayanai kan cewa 'yan Najeriya na ta kokarin haddace sabon taken, rahoton TVC
Sai dai duk da kokarin, sun koka kan rashin samun cikakken bayani da kuma samun taken da aka tace.
Bayan tattara korafin da jama'a suka shigar hukumar NOA ta ce a yanzu haka tana tattaunawa kan gyare-gyaren da za ayi domin wayar da kan al'umma.
Ta kuma yi kira ga jami'an gwamnati idan za su yi amfani da taken su tuntubi jami'an NOA domin samun asalin taken a wajen su.
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe za ta gina titi mai tsawon kilomita 18 kan kudi naira biliyan 20 a fadin jihar.
Gwamnatin ta ayyana titin asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya zuwa kolejin ilimi da fasaha da ke cikin garin cikin inda aikin zai shafa.
Asali: Legit.ng