Home Back

Makarantar gwamnati da iyaye ke ɗaukar malamai aiki a Kano

bbc.com 2024/7/3
Hoton makarantun gwamnatin Kano
Bayanan hoto, Hoton makarantar gwamnati a Kano da dalibi ke koyo a cikin wahala
  • Marubuci, Abubakar Maccido
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
  • Aiko rahoto daga Kano State, Nigeria

Makarantar Sakandaren Ƴanmata ta Gwamnati (GGSS) da ke ƙauyen Tsakuwa a karamar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano na fama da rashin malaman da za su koyar da yara, lamarin da ya tilasta wa mazauna ƙauyen da wata gidauniya ta tara kuɗi domin ɗaukar malaman da za su koya wa ɗaliban makarantar karatu.

GGSS Tsakuwa, makarantar ƙauyen da ta shafe sama da shekaru 14 tana fuskantar ƙarancin malamai da kayan aiki da kujerun zama da dai sauransu.

Makarantar na da ɗalibai aƙalla 800, amma duk suna fuskantar matsalar ƙarancin malamai.

Haka kuma, adadin malaman gwamnati na makarantar bai wuce takwas ba, kuma a wasu lokutan yara kan je makaranta ba tare da sun samu malaman da za su koyar da su ba.

Don haka ne mutanen ƙauyen suka samar da wata gidauniya mai suna Tsakuwa Mu Farka, kuma wannan gidauniyar ce take ɗaukar nauyin malaman da aka dauka domin koyarwa a makarantar.

'Mun tuntuɓi gwamnati amma abin ya ci tura'

Abdullahi Yusuf shi ne shugaban gidauniyar Tsakuwa Mu Farka mai kula da harkokin ilimi na ƙauyen kuma ya bayyana irin wahalhalun da suka fuskanta wajen ƙoƙarin shawo kan matsalar ta hanyar aika wasika ga gwamnatin Kano domin inganta harkar ilimin makarantu, amma duk ƙoƙarinsu yana cin tura.

Ya ce bayan korafe-korafen da suka yi wa gwamnati, har yanzu ba a ba su amsa ba wanda hakan ya sa suko ƙirƙiro gidauniyar da za ta inganta ilimin ɗaliban ƙauyensu.

Gidauniyar Tsakuwa Mu Farka ta ɗauki malamai 16 a lokacin da suka fara aiki a shekarar 2021 domin taimaka wa ɗaliban, inda ta rika biyan su naira 10,000 duk wata.

“A lokacin da gidauniyar ta fara aiki, mun ɗauki malamai 16 domin su taimaka wa makarantar GGSS da ke Tsakuwa, saboda wasu lokuta yara kan je makaranta su dawo ba tare da an koya musu komai ba." in ji Yusuf.

"Yanzu kamar yadda nake magana da ku makarantunmu ba su da isassun malamai da kayan aiki kamar kujerun zama dai sauran su," kamar yadda shugaban gidauniyar ya ƙra da cewa.

“Daga asusun gidauniyarmu da muku ƙirƙiro shekaru uku da suka gabata ne muke biyan malaman da aka ɗauka aiki, muna samun kuɗin ne daga hannun waɗanda ke cikin gidauniyar da kuma iyayen yara a ƙauyen namu,” inji Yusuf.

"Wani lokaci idan muka yi magana da mutum ɗaya sai mu ce masa a wannan watan za ka biya malami ɗaya ko biyu daga aljihunka ." Yusuf ya ƙara da cewa.

Ya kara da cewa a bana an ɗauki malamai 10 waɗada za su taimaka wajen koyar da ɗaliban, wanda ke nufin cewa malamai 26 ne aka ɗauka aiki gaba daya.

Hoton makarantar GGSS
Bayanan hoto, Hotunan azuzuwan koyarwa na makarantar GGSS Tsakuwa, Jihar Kano
Foto of Kano school
Bayanan hoto, Hotunan azuzuwan koyarwa na makarantar GGSS Tsakuwa, Jihar Kano

Wasu malaman sa-kai da BBC ta zanta da su, sun bayyana cewa suna yin wannan aiki ne domin su bayar da tasu gudummawar ga ilimin yaran ƙauyen, duk da cewa kuɗin da ake ba su bai kai taka kara ya karya ba.

Ɗaya daga cikin malaman, Ibrahim Alhaji Hamisu ya ce, “Na yi wannan aiki tsawon shekara uku, kuma ina yin hakan ne ba don kudin aikin ko kudin da ake ba ni ba, sai dai don in taimaka wajen koyar da yara, domin ina ganin su a matsayin ƙannaina kuma su ma idan sun girma za su yi abubuwan da suka ga muna yi ko sama da haka."

"Kafin in na fara koyarwa, gidauniyar Tsakuwa Mu Farka ce ta sanya ni wajen samun horo kan dubarun koyarwa saboda na ƙware," in ji Hamisu.

Fatima Auwal Idris ta ce ta fara wannan aiki ne shekaru uku da suka wuce, kuma ana biyan ta Naira 5,000 duk wata.

“Na fara wannan aiki ne shekaru uku da suka wuce bayan an kafa gidauniyar Tsakuwa Mu Farka, kuma ana biya na naira 5,000 duk wata, ina yin wannan aikin ne domin kaina kuma na ce tunda gwamnati ba ta samar mana da malamai ba, dole mu tashi tsaye da kanmu mu taimaka wa kanmu da sauran matasa"

"Na kuma yi imanin cewa irin wannan aikin sa-kai da muke yi zai sa gwamnati ta taimaka mana ta hanyar samar mana da malamai da yawa."

“Ina fata wata rana gwamnati za ta dube mu ta tura malamai makarantunmu da ke kauyen nan,” in ji Fatima.

Iyaye a ƙauyen na Tsakuwa sun nuna rashin gamsuwa da halin da ƴaƴansu ke ciki a makarantun garin.

Sani Bala, wanda ke da yara huɗu a makarantar ya ce, “Abin takaici ne a gare mu a ce a makarantun gwamnati ba mu da isassun malamai, har ta kai ga muna karɓar kuɗi daga aljihunmu muna biyan malaman sa-kai da muka ɗauka aiki."

Bala ya ce "Yaranmu a ƙasa suke zama domin a koyar da su saboda babu kujerun zama a azuzuwa."

Shi ma Salisu Idiris ya bayyana alhininsa tare da yin kira ga gwamnatin Kano da ta ɗauki mataki tare da bayar da taimako a harkar ilimi ga ƙauyen.

“Ba za mu iya bayyana takaicinmu gaba ɗaya ba, amma kiran da muke yi ga gwamnati shi ne ta samar da malamai ga makarantunmu waɗanda za su koyar da ƴaƴanmu,” inji shi.

“Ilimi na da matuƙar muhimmanci, shi ya sa muka fara tara kuɗi a ƙauyen domin biyan malaman sa-kai da ke koyar da ƴaƴanmu a makarantar”.

Amma har zuwa lokacin da muka haɗa wannan rahoto, BBC ta yi kokarin jin ta bakin kwamishinan ilimi na jihar Kano ta hanyar aika sako da kuma kiran waya kan wannan batu, amma bai amsa ko ɗaya ba.

Ƙofar shiga makarantar GGSS Tsakuwa da dalibai ke fuskantar mawuyacin hali don koyo
Bayanan hoto, Ƙofar shiga makarantar GGSS Tsakuwa, Kano State
People are also reading