Home Back

'Yan Bindiga Kai Hari Ido Na Ganin Iso, Sun Kashe Bayin Allah Ranar Yawon Sallah a Arewa

legit.ng 2024/7/1
  • Ƴan bindiga sun kashe mutane yayin da suke tsaka da taro a kauyen Ewehko, ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige akalla mutum biyar har lahira ido na ganin ido ranar Litinin
  • Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto domin gano ragowar waɗanɗa suka ɓata sakamakon harin, ƴan sanda ba su ce komai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Mutane sun shiga tashin hankali da fargaba bayan wasu ƴan bindiga sun kai farmaki kauyen Ewehko da ke yankin ƙaramar hukumar Kajuru a Kaɗuna.

An tataro cewa maharan sun bindige mutanen kauyen har lahira a lokacin da suna cikin yin wani taron manyan gari.

Malam Uba Sani.
Yan bindiga sun kashe mutane da tsakar rana a jihar Kaduna Hoto: Senator Uba Sani Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ci karo da hotunan waɗanda ƴan bindigar suka kashe da kuma.baburan da suka ƙona yayin harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu majiyoyi daga ƙauyen sun bayyana cewa maharan sun ƙona baburan wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:14 na rana a washe garin Sallah watau ranar Litinin, 17 ga watan Yuni, 2024.

Wani mazaunin garin da ya bayyana sunansa da Bilyaminu Maro ya ce an gano gawarwakin mutane biyar daga wurin da lamarin ya faru.

"Lamarin ya faru da misalin karfe 2:14 na tsakar rana, zuwa yanzu da nake magana da ku mun gano gawarwakin maza huɗu da mace ɗaya.

"Muna ci gaba da bincike a wurin da kuma cikin jeji domin zaƙulo sauran waɗanda suka ɓata," in ji shi.

Wani mazaunin garin, Reuben Maro, ya ce maharan sun kuma kona gidaje, ciki har da baburan mutanen da suka kashe.

Ya ce ƴan ta'addan sun farmaki mutane ido na ganin ido da tsakar rana, suka aikata mummunan nufinsu.

Har yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna da hukumar ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

A wani rahoton kuma jirgin yaƙi ya kai samame sansanin ƴan bindiga, ya yi nasarar hallaka aƙalla ƴan ta'adda 100 a yankin ƙaramar hukumar Faskari.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula ya ce sojojin sun lalata babura sama da 45 da wasu kayan aikin ƴan bindigar

Asali: Legit.ng

People are also reading