Home Back

Hukumar EFCC ta Damke Mata da Surukarta Bisa Zambar Makudan Kudi

legit.ng 2024/7/5
  • Hukumar EFCC ta kama wata Blessing Nchelem da surukarta Deborah Jack bisa zargin zambar kudin wasu filaye da ba nasu ba akan N6m
  • An kama su ne a birnin Port Harcourt dake jihar Rivers da zargin zambatar Senibo Richmond Opusunju kan cewa za su sayar muasa da filaye guda uku
  • Mai shari’a P. I. Ajoku ta tisa keyarsu gidan gyaran hali da tarbiyya yayin da ta umarci lauyansu S. O. Aburu ya nemi beli a rubuce ba da baki ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Rivers- Hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC) ta bayyana cafke wasu mata Blessing Nchelem da surukarta Deborah Jack tare da gurfanar da su gaban kotu.

An kama su a jihar Port Harcourt dake jihar Rivers bisa zargin zambar kudin fili N6m, tare da gurfanar da su gaban babbar kotun tarayya karkashin mai shari’a P. I. Ajoku.

Hukumar EFCC
An kama Blessing Nchelem da Deborah Jack bisa zambar N6m Hoto: Economic and Financial Crimes Commission Asali: Facebook

EFCC da ta wallafa hakan a shafinta na facebook ta bayyana cewa ana zargin mutanen da kokarin damfarar wani Senibo Richmond Opusunju kudi N6m na kudin filayen uku da ba nasu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane laifi ake zarginsu da shi?

Hukumar EFCC ta kama wasu mata biyu bisa zargin zambar kudin filaye, tare da hada kai domin aikata laifi, karbar kudi ta hanyar zamba, da kuma adana kudin haramun da yawansu ya kai N6m.

Da aka karanto musu laifukansu, matan sun musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi musu, inda nan take lauyansu S. O. Aburu ya roki kotu ta bayar da belinsu, kamar yadda Punch ta wallafa.

Amma lauyoyin EFCC sun nemi kotu da kada ta bayar da belinsu, a kuma Sanya ranar fara sauraron shari’ar tare da tisa keyarsu zuwa gidan kaso.

Mai shari’a Ajoku ta ki bayar da belin mutanen biyu, sannan ta umarci lauyansu ya nemi belin a rubuce a zaman a gaba.

EFCC ta kama matashi a Gombe

A wani labarin kuma kun ji cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta damke wani matashi a jihar Gombe bisa zargin cin zarafin Naira.

An cafko matashin ne bayan an gano shi yana lika N200 a wani gidan rawa, kuma EFCC ta tabbatar da sai ta hukunta da shi domin dakile faruwar haka a gaba.

Asali: Legit.ng

People are also reading