Home Back

Ministan tsaron Israila ya yi barazanar ficewa daga gwamnatin Israila

bbc.com 2024/6/26

Asalin hoton, Getty Images

Ganntz
Bayanan hoto, Benny Gantz

Ministan yakin Israila Benny Gantz ya yi barazanar yin murabus daga majalisar yakin kasar idan Firai ministan Benjamin Netanyahu ya ki bayyana shirinsa na kula da zirin Gaza bayan yakin da suke yi da Hamas yazo karshe.

Mista Gantz ya debarwa gwamnatin Israila wa‘adin ranar 8 ga watan Yuni domin ta tsara manufofi 6 ciki har da kawo karshen mulkin Hamas a Gaza da kuma kafa gwamnatin farar hula ta kasa da kasa.

Ministan ya yi wannan barazanar ce a taron manema labarai:

''Mutane Israila suna kallon ka, dole ne ku zabi tsakanin kishin kasa da son zuciya dole ne ku zabi tsakanin hadin kai da bangaranci, dole ne ku zabi tsakanin abin da ya kamata da kuma rashin bin doka da oda da kuma nasara da bala'i''

'' Idan aka sa kasar a gaban son rai kuma gwamnatin kasar ta yanke shawarar bin sahun shugabaninta na baya irinsu Herzl da Ben Gurion da Begin da kuma Rabin, to zamu kasance cikin kawancen gwagwarmaya amma idan ku ka zabi hanyar masu tsatsauran ra’ayi kuma ku ka jagoranci kasar ta fada cikin balai to za mu fice daga cikin wannan gwamnati ta hadin gwiwa' in ji shi

'

Sai dai Mista Netanyahu ya yi watsi da kalaman a matsayin ‘’kalmomi barazana’’ wandanda za su sa ‘’ Israila ta sha kaye’’

Rikicin siyasa da ke ci gaba da ruruwa dangane da alkiblar yakin Gaza na zuwa ne a dai dai lokacin da ake gwabza fada tsakanin bangarorin biyu inda sojojin Israila suka kutsa cikin Jabalia da ke kusa da garin Gaza watau daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira mai tarihi na yankin kuma yanki ne da a baya sojojin Israila suka ce sun murkushe mayakan Hamas.

Kalaman na Mista Gantz na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani mamba a majalisar ministocin yakin kasar , watau ministan tsaro Yoav Gallant ya nemi Mista Netanyahu ya bayyana a fili cewa Israila ba ta da wani shiri na karbe mulkin farar hula da na Soja a Gaza.

Mista Gallant ya ce ya sha tabo batun na tsawon watanni amma bai samu amsa ba.

Shi da Misra Gantz sun ce idan sojoji suka ci gaba da iko da Gaza to wannan zai kara jefa kasar cikin hadari ta fusknar tsaro yayin da wasu har da mambobi masu ra’ayin rikau a cikin gwamnatin hadaka ta Mista Netanyahu na ganin ya zama dole a ci gaba da rike madafun iko domin murkushe Hamas.

People are also reading