Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Sa Almajirai Da Yara Fiye Da Miliyan 2 A Karatun Boko

leadership.ng 2024/5/17
Gwamnatin Tarayya Ta Sa Almajirai Da Yara Fiye Da Miliyan 2 A Karatun Boko

Gwamnatin tarayya ta sa yara Almajirai fiye da miliyan biyu a makarantar Firamare da koyon Larabci a cikin wata shida.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka; a lokacin da aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin Ilimi a Nijeriya, ranar Talatar da ta gabata a Abuja.

Farfesan, ya ce babban abin da ma’aikatar iliminn za ta fi bai wa muhimmanci shi ne, samar da sahihan alkalumma a bangaren, don ci gaban ilimin yara da kuma fasahar koyon abubuwa daban-daban, a haka ne za a iya rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Har ila yau, don kokarin samun nasarar lamarin; ma’aikatar ilimin ta yi tsari mai matukar kyau, wanda aka yi wa lakabi da ‘Tsarin bangaren Ilimi na Nijeriya daga shekarar 2024 zuwa 2027’.

Ministan ya kara da cewa, “Aiwatar da umarnin shugaban kasa ne, ya sa muka gana da masu ruwa da tsaki; don tattauna ci gaban da aka samu dangane da shawarwari 23 da muka cimma.

Haka zalika, daya daga cikin manufofin gwamnati shi ne; kokarin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, wannan dalili ne yasa gwamnati ta himmatu wajen ba wa al’amarin muhimmanci yadda ya kamata.

“Abubuwan da muke bayana sune, irin gudunmawar da hukumomin da ke karkashin ma’aikatar Ilimi ke bayarwa, don kokarin tabbatar da an yi maganin wannan matsala.

Da yake bayani a kan garkuwar da aka yi da daliban Jami’ar Kalaba, Ministan ya ce; ma’aikatar ilimi na aiki tare hukumomin tsaro, domin kokarin samun kubuto da wadannan daliban, sannan kuma hukumar kula da manyan makarantu, ta gina wa jami’ar katanga.

Shi ma a nasa bangaren, Karamin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Sununu ya bayyana kokarin da ma’aikatar ilimi ta yi na shigar da tsarin fasaha a harkar ta Ilimi tare da bunkasa koyon sana’o’i ta bangarori daban-daban.

Sununu ya kara da cewa, hakan zai yi maganin matsalar koyarwa da ake fuskanta a kananan makarantu.

Sannan ya kara jaddada cewa,“Mun sani ko shakka babu, akwai bukatar samar da babbar tawaga wajen maganin matsalolin da ake fuskanta a bangaren ilimi.

Da yake ilimi babban ginshiki ne na rayuwa Dan Adam, al’umma, kasa da kuma duniya baki-daya, shi yasa bai kamata a mayar da shi Saniyar ware ba”.

“Ganin muhimmancin lamarin ne ya sa kungiyar kwadago ta kasa da kasa ta bayyana Ilimi a matsayin kamar wani kaya, da za a iya shigowa da shi, don haka akwai bukatar hadin kan gida da waje; domin cimma wannan buri”.

A nasa banagaren, Kwamishinan Ilimi na Jihar Legas, Jamiu Alli-Balogun ya nuna rashin jin dadinsa da hukumar shirya jarrabawa ta Afirka ta yamma, sakamakon karin kudi da ta yi zuwa Naira 27,000, wanda mafi yawancin iyaye ba za su iya biyan wannan kudi ba.

People are also reading