Home Back

Batun 'yan gudun hijirar Afghanistan ya kankane zaɓen shugaban ƙasar Iran

bbc.com 3 days ago
Afghan refugees walk with their belongings after being deported back from Iran at the Islam Qala Border between Afghanistan and Iran, in Herat province on 30 May 2024

Asalin hoton, AFP/Getty Images

  • Marubuci, Ali Hussaini and Zainab Mohammadi
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian

“A ƴan watannin baya-bayan nan, yanayin - da halastattu da 'yan gudun hijirar da ke zaune ba bisa ƙa'ida ba a Iran - babu daɗin ji.

Ko a kan hanya ka ga ɗan gudun hijira za ka iya gane halin da yake ciki na rashin jin daɗi. An tsananta kamen 'yan gudun hijirar da ke zaune ba bisa ƙa'ida ba. A yanzu da muka zama wani batu da ya kankane zaɓen ƙasar, abubuwa za su sake taɓarɓarewa.”

Wannan shi ne saƙon wani mai sauraron sashen fasha na BBC a Afghanistan, a lokacin da aka buƙaci ya bayyana ra'ayinsa kan yadda zaɓen shugaban Iran zai shafi miliyoyin 'yan gudun hijirar Afghanistan da ke zaune a ƙasar.

Ma'aikatar harkokin cikin ƙasar ta ce akwai 'yan Afghanistan fiye da miliyan biyar da ke zaman gudun hijira a Iran.

Duk da cewa sun shafe gomman shekaru suna zaune a ƙasar, batun 'yan gudun hijirar Afghanistan a Iran ya shiga cikin batutuwan da aka fi muhawara a kansu a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe.

A karon farko 'yan takara sun yi muhawara mai zafi game da batun, gabanin zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar yau 28 ga watan Yunin da muke ciki.

'Yan gudun hijirar Afghanistan a Iran

Akwai dubban ɗaruruwan 'yan gudun hijirar Afghaninstan da suka shafe fiye da shekara 40 a Iran, da yawa daga cikinsu sun hayayyafa.

To amma duk da wannan jimawa da suka yi a ƙasar, har yanzu ana yi musu kallon 'yan gudun hijira, saboda ba a ba su takardun izinin zama 'yan ƙasar ba.

Iran ƙasa ce da ba ta son zaman 'yan gudun hijira a cikinta, saboda yadda take fafutikar magance matsalolin tattalin arzikinta.

To sai dai ana ganin barin miliyoyin 'yan gudun hijirar Afghanistan da ta yi a matsayin wata alama ta nuna jin ƙai ga maƙwabciyar tata da yaƙi ya ɗaiɗaita.

A lokacin da sojoji tarayyar Soviet suka mamaye Afghanistan a 1979, domin taimaka wa gwamnatin da ke goyon bayan tarayyar, a yaƙin da take yi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Aƙalla sojojin tarayyar Soviet 100,000 ne suka kwashe kusan shekara 10 suna yaƙi a ƙasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 15,000.

Kusan 'yan Afghanistan miliyan guda aka kashe a lokacin yaƙin, aka kuma jikkata wasu, yayin da wasu miliyoyi suka bar muhallansu zuwa wasu ƙasashen kamar Iran da Pakistan.

Shugaban Amurka na wancan lokacin, Jimmy Carter, ya ce mamayar da tarayyar Soviet ta yi wa Afghanistan barazana ce ga Iran da Pakistan.

Tun daga lokacin ne kuma rashin zaman lafiya da gaba suke ta ƙaruwa, lamarin da ya tilasta ci gaba da samun 'yan gudun hijirar. Hakan ne kuma ya sa ba za a iya tantance haƙiƙanin adadin 'yan gudun hijirar Afganistan a Iran ba.

Bayan da Taliban ta sake ƙwace mulkin Afghanistan a shekarar 2021, 'yan ƙasar da dama sun koma Iran, kamar yadda wasu da suka kwashe gomman shekaru a can suka bayyana.

Hukumomin Iran na samun saɓani wajen bayyana adadin 'yan Afghanistan da ke zaune a ƙasar, inda alƙaluman ke farawa daga miliyan biyar zuwa bakwai.

Idan muka yi la'akari da yawan al'ummar Afghanistan na kusan miliyan 40 (adadin da ba za a iya tantancewa ba), to za mu iya cewa mutum guda cikin bakwai na 'yan Afghanistan na gudun hijira a Iran.

Ƙaruwar 'yan Afghanistan a Iran ya sa wasu Iraniyawan na nuna adawarsu da hakan, kuma yayin da ƙasar ke fama da takunkumai da matsin tattalin arziki, Iraniyawan na kallon 'yan gudun hijirar a matsayin ma'aikatan da za su riƙa yi musu leburanci cikin rahusa.

Hakan ne ya sa suke ɗaukar su aikatau ba tare da inshora ba, sannan suke biyan su kuɗi ƙalilan idan aka kwatanta da yadda suke biyan 'yan ƙasar.

'Matsalar tsaro'

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Vehicles move past a billboard displaying the faces of the six candidates running in the upcoming Iranian presidential election in Valiasr Square in central Tehran on 15 June 2024 (
Bayanan hoto, Wasu daga cikin 'yan takarar shugabancin ƙasa na sanya batun 'yan gudun hijirar cikin batutuwan yaƙin neman zaɓensu.

Kusan shekara biyu kenan da wani ɗan gudun hijirar Afhanistan mai bin aƙidar Sunni ya farmaki wasu Iraniyawa 'yan Shi'a uku da wuƙa a masallacin Imam Reza, wuri mafi tsarki ga mabiya Shi'a a arewa maso gabashin Iran, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar biyu daga cikinsu.

Wannan lamari ya nuna yadda girman matsalar tsaro da 'yan gudun hijirar Afghanistan ke haifar wa Iran baya ga matsalar tattalin arziki da laifukan da suka shafi zamantakewa.

A shekarun baya-bayan nan, Khosan - wadda reshe ce ta ƙungiyar IS da aka fi sani da IS-K - ta kai munanan hare-hare aƙalla biyu a Iran.

An ce ƙungiyar IS-K na da matsuguni ne a Afghanistan, inda take shirya hare-harenta tare da aika mayaƙanta don kai hare-haren.

Damuwar da Iraniyawa ke da ita kan hakan ne ya sa suka yi ta kiraye-kirayen fitar da 'yan gudun hijirar daga ƙasarsu, lamarin da ya kai su ga shirya gangami musamman a shafukan sada zumunta.

Kuma a karon farko, 'yan takarar shugabancin ƙasar suka fara ambata batun 'yan gudun hijirar a lokutan gangamin yaƙin neman zaɓensu.

'Gina katangar kan iyaka’

Ɗaya daga cikin 'yan takarar, Mohammad Baqer Qalibaf - tsohon kakakin majalisar dokokin ƙasar har sau biyu - ya bayyana a wani gangamin yaƙin neman zaɓe cewa zai gina katanga a kan iyakar gabashin ƙasar da Afghanistan da kuma Pakistan don tabbatar da tsaro.

Mista Qalibaf ya ce '' 'yan gudun hijirar da ke shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba su ne tushen matsalolin da ƙasar ke fuskanta, kamar safarar ƙwayoyi da rashin aikin yi da yawan sakin aure''.

Don haka ya ce zai magance matsalar kwararar 'yan gudun hijira zuwa ƙasar, musamman daga yankin gabashin ƙasar.

Shi kuwa Masoud Pezeshkian, da ake kallo a matsayin ɗan takarar mai matsakaicin ra'ayi, ya bayyana a shafinsa na X cewa zai rufe kan iyakokin ƙasar, domin hana ƙarin 'yan gudun hijirar Afghanistan shiga ƙasar.

Ya kuma amince cewa da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar Afghanistan na taka muhimmiyar rawa wajen taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar.

Ya kuma ce zai duba batun tattaunawa da su da kuma daidaitawa da ƙasashen Turai don su karɓi wasu daga cikinsu, ko su bai wa ƙasar tallafin kuɗin kula da su, sai dai bai bayyana yadda zai yi shirin ba.

'A kullum muna fargabar fitar da mu’

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Afghans forcibly deported back from Iran to Afghanistan walk towards the border between Afghanistan and Iran at Islam Qala port in October 2021
Bayanan hoto, 'Yan gudun hijirar na rayuwa cikin fargabar fitar da su

Yadda batun 'yan gudun hijirar Afganistan ya shiga cikin batutuwan yaƙin neman zaɓen shugaban Iran, ya haifar da damuwa tsakanin 'yan gudun hijirar.

Ɗaya daga cikin 'yan gudun hijirar ya ce da alama 'yan takarar shugaban ƙasar Iran ba su da wani kyakkyawan shiri kan 'yan gudun hijirar.

Ya ce yadda 'yan takarar ke furta kalamai marasa daɗi kan 'yan gudun hijirar na ''ƙarfafa wa masu tsattsauran ra'ayi da masu wariyar launin fata gwiwa, tare da haifar da tsoron 'yan gudun hijirar tsakanin Iraniyawa, lamarin da ke sanya rayukansu cikin hadari''.

Shi ma wani ɗan gudun hijirar ya faɗa wa BBC cewa: ''duk abin da ke faruwa a ciki da wajen Iran na shafar rayukan 'yan Afghanistan a Iran, ɗan'uwana da aka haifa a Iran, a yanzu yana ƙoƙarin tafiya Turai ta hanyar da ba ta dace ba''.

''Ba mu da damar komawa Afghanistan, haka kuma ba mu da kyakkyawar makoma a Iran, ina da digiri na biyu a fannin nazarin lantarki. A baya ni da matata muna koyarwa a jami'ar Afghanistan, amma bayan dawowar Taliban dole muka bar ƙasar, a yanzu matata aikin leburanci take yi a Iran, a kullum muna fargabar fitar da mu daga ƙasar, me ya sa aka hana mu samun ingantacciyar rayuwa''?

'Yan gudun hijirar Afganistan da suka shafe gomman shekaru a Iran na fuskantar tarin matsaloli, misali an ɗauki lokaci mai tsawo ba a sayar musu layin waya domin su saka a wayoyinsu, to amma a yanzu za a iya sayar musu, sai dai ba abu ne mai sauƙi ba.

Mafi yawan 'yan Afghanistan da ke sauraron sashen fasha na BBC sun jadda a cikin saƙonninsu cewa babu wanda ya je Iran bisa raɗin kansa, ''tilas ce'' ta sa muka je Iran''.

Ɗaya daga cikinsu - wadda ɗaliba ce - ta ce tana fargabar komawa Afghanistan da a yanzu ke ƙarƙashin mulki da ke tauye wa mata 'yanci a kowace rana.

Ta ci gaba da cewa ''Idan ba za su bari mu zauna a ƙasarsu ba, muna fatan wasu ƙasashe su ba mu mafaka, saboda a kullum wulaƙanci muke fuskanta a Iran.''

People are also reading