Home Back

Rasuwar Suruka: Gwamnoni Sun Kai Wa Shettima Ziyarar Ta’aziyya

leadership.ng 2024/7/6
Rasuwar Suruka: Gwamnoni Sun Kai Wa Shettima Ziyarar Ta’aziyya

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya jagoranci takwarorinsa wajen ziyarar ta’aziyyar ga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, bayan dawowarsa birnin tarayya Abuja, a ranar Laraba.

Gwamnonin, sun yi addu’ar Allah ya jiƙan surukar mataimakin shugaban ƙasa, marigayiya Hajiya Maryam Albishir, ya kuma bai wa iyalanta haƙurin jure rashinta.

Da yake godiya da ziyarar, mataimakin shugaban ƙasar, ya nuna jin daɗinsa kan ta’aziyar da gwamnonin suka kawo da yadda suka nuna tausayi da goyon baya gare shi.

Shettima ya yaba da haɗin kan Gwamnonin da Gwamnatin Tarayya ya kuma yi kira da a ƙara ba da hadin kai da goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu, domin cimma manufofinsa da na ƙasa baki daya.

People are also reading