Home Back

Gwamantin Tarayya da Fadi Matakan da Ta Dauka Domin Rage Hauhawar Farashin Abinci

legit.ng 2024/6/26
  • Yayin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara kan mulki, jami'ansa sun fara bayyana irin kokarin da suka yi
  • Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya fadi matakan da ma'aikatarsa ta dauka domin shawo kan matsalolin tsadar abinci
  • Sanata Kyari ya kuma bayyana yadda ma'aikatar noma ta kasa ta samar da N309b domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Ministan harkokin noma, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana nasarorin da ma'aikatarsa ta samu cikin shekara daya.

Ministan noman ya bayyana haka ne a wani taron baje kolin nasarorin da gwamnatin Bola Tinubu ta samu cikin shekara daya.

Sanata Kyari
Gwamnatin tarayya ta dauki matakin rage tsadar abinci. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum. Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministan ya kara bunkasa ayyukan nomar rani sosai musamman a yankin Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin rage tsadar kayan abinci

Sanata Kyari ya ce sun samar da ingantaccen ton 60,432 na iri domin bunkasa harkar noma wanda hakan zai rage tsadar abinci a Najeriya.

Ya kara da cewa sun samar da maganin kwari lita 501,726 da taki ton 62, 328.5 duk domin saukakawa da bunkasa noma a Najeriya.

A bangaren kiwo kuma minisan ya ce sun samar da dam takwas da borehole biyu da wuraren tattara madarar shanu 164 da sauransu domin wadatar da abinci.

A cewar ministan, idan noma ta bunkasa ana sa ran farashin abinci ba zai yi mummunan tashi a kasuwanni ba.

Yadda noma ta bunkasa tattalin Najeriya

Ministan ya bayyana cewa sun kaddamar da noman rani a jihohi 15 a fadin Najeriya inda aka noma shekta sama da 118,675 na alkama, rahoton Vanguard.

Ya ce jihar Jigawa kawai ta samar da alkama sama da ton 50,000. Wanda idan aka hada lissafa nomar alkamar kawai ta samar da kudi kimanin N309b ga Najeriya.

Atiku ya soki salon mulkin Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bayyana dalilan da suka hana shugaban kasa Bola Tinubu cin nasara cikin shekara daya.

Atiku Abubakar ya yi bayanin ne a lokacin da yake sharhi kan yadda jam'iyyar APC mai mulki ta gudanar da mulki bayan samun nasara a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

People are also reading