Home Back

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Naira 62,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

leadership.ng 2024/6/18
Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC

Bayan ganawar sa’o’i da aka yi a ranar Juma’a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, gwamnatin ta yi karin kan sabon mafi karancin albashi daga Naira 60,000 zuwa Naira 62,000.

Sai dai kungiyar kwadagon ta bukaci a biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin albashin daga abin da ya bukata a baya Naira 494,000.

Idan ba a manta ba, bayan cikar wa’adin sa’o’i 48 da shugaban kasa, Bola Tinubu ya bai wa ministan kudi, Wale Edun, ya gabatar wa shugaban sabon tsarin mafi karancin albashin.

Sanarwar na zuwa ne kwanaki biyu bayan Tinubu ya bayar da umarnin gabatar da sabon tsarin mafi karancin albashi da kuma nazarin abin da ke tattare da shi.

Rahoton na ministan kudi an ce zai zayyana wasu sabbin matakan mafi karancin albashi tare da tasirin kasafin ga gwamnatin tarayya.

Idan ba a manta ba, kungiyar kwadago ta fara yajin aiki a fadin kasar nan a Litinin, domin neman karin mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnati.

A gefe guda kuma ma’aikatan na bukatar janye karin kudin wutan lantarki da aka yi a baya-bayan nan.

Shugabannin kungiyoyin kwadagon NLC da TUC, sun dakatar da aikin na tsawon kwanaki biyar bayan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin tarayya domin ci gaba da tattaunawa, tare da nemo sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikatan.

People are also reading