Home Back

Yaron Sanusi II Yayi Magana da Kotu Ta Saurari Shari’ar Aminu Ado Bayero

legit.ng 2024/10/4
  • Ashraf Sanusi Lamido Sanusi ya yi tsokaci a lokacin da ake shari’a da gwamnatin jihar Kano a kan rikicin masarauta
  • Yaron Mai martaba Muhammadu Sanusi II yana ganin babu ta inda gwamnati ta toye hakkin Alhaji Aminu Bayero bayan tsige shi
  • Bayan an gama sauraron kowane bangare a shari’ar, an yi hukuncin da ya sabawa tunanin Ashraf Sanusi Lamido Sanusi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Bayan tsawon lokaci ana jiran kotu ta yi hukunci, a karshe alkali kawo shari’ar rikicin masarautar Kano.

Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya kalubalanci sauke sarki Aminu Ado Bayero daga karaga.

Ashraf Sanusi Lamido Sanusi ya tofa albarkacin bakinsa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter bayan an yi hukunci.

Sarkin Kano
Ana shari'a a kotu da Sarkin Kano Hoto: @HrhBayero, @SanusiSnippets Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Ashraf Sanusi Lamido kamar yadda ya saba, ya tsoma baki a shari’ar da za a iya cewa babu wanda ya yi nasara.

Duk da kotu ta ce ta na da hurumin sauraron karar, Aminu Ado Bayero, da alama dai Ashraf yana da ja a kan matsayar.

Yaron Sarkin ya nuna cewa ba a toyewa Alhaji Aminu Ado Bayero hakkin zama ‘dan kasa ba dominyin sarauta gata ce.

“Ko mutum bai je makarantar koyon shari’a ba, ya san babu wani ‘hakki’ a zama Sarki.”
“Akwai hakkokin rayuwa, tunani, yawo da sauransu, wadannan su ne ainihin hakkoki,”
“Kuma a cikinsu babu wanda aka toye masa (Mai martaba Aminu Ado Bayero).”

- Ashraf Sanusi Lamido

A zancen da ya yi a shafinsa, Ashraf Sanusi ya yi magana a kaikaice game da fadar Nasarawa da basaraken yake zama.

Abin da ya ke nema ya nuna shi ne Sarkin Kano na 15 ya shiga hurumin da ba na shi ba.

A karshe alkali ya ci gwamnatin Kano tarar N10m kan take hakkin Aminu Ado Bayero wajen maido Muhammadu Sanusi II.

Babu mamaki Ashraf wanda ma’aikacin banki ne kuma masani a ilmin tattalin arziki bai yi tunanin haka shari’ar za ta kaya ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading