Home Back

Moise Kean ya koma Fiorentina daga Juventus

bbc.com 2024/8/21
Moise Keane

Asalin hoton, Getty Images

Fiorentina ta kammala ɗaukar Moise Kean daga Juventus, kamar yadda dukkan ƙungiyoyin da ke buga Serie A suka sanar ranar Talata.

Juventus za ta karɓi $14.1 da karin Yuro miliyan biyar ƙudin tsarabe-tsarabe , amma ba su fayyace tsawon ƙwantiragin da Kean ya amince da shi ba.

Mai shekara 24, wanda ya buga wa tawagar Italy wasa 15 da cin ƙwallo hudu ya kuma taka leda a Paris St Germain da Everton.

Kean ya fuskanci kalubale a Juventus, wanda bai ci ƙwallo ba, amma ya bayar da ɗaya aka zura a raga.

Fiorentina ta kare a mataki na takwas a Serie A da ta wuce, wadda ta yi ta biyu a UEFA Conference League karo biyu a jere.

People are also reading