Home Back

Gwamna PDP Ya Zama Na 2 Wurin Kara Mafi Karancin Albashi Ga Ma'aikata, Ya Ba Su Hakuri

legit.ng 2024/5/20
  • Yayin da ake bikin ranar ma'aikata a Najeriya, gwamnan jihar Kuros Riba ya amince da sabon mafi karancin albashi
  • Gwamna Bassey Otu ya amince da biyan N40,000 ga ma'aikatan jihar inda ya ce sun yi karin ne duba da halin da jihar ke ciki
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Godwin Obaseki ya amince da mafi karancin albashi har N70,000 a jihar Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Cross River - Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba ya amince da karin mafi karancin albashi ga ma'aikata jiharsa.

Otu ya amince da biyan N40,000 ga ma'aikatan jihar inda ya ce ya yi hakan duba da halin da ake ciki.

Gwamnan PDP ya kara mafi karancin albashi ga ma'aikata
Gwamna Bassey Otu na Kuros Riba ya amince da N40,000 a matsayin mafi karancin albashi. Hoto: Bassey Otu. Asali: Facebook

Wane alkawari Gwamna Otu ya yi?

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin bikin ranar ma'aikata a yau Laraba 1 ga watan Mayu a birnin Calabar, Cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba ba ma'aikata kulawa na musamman wurin biyan albashi da fansho da kuma sauran hakkokinsu.

"Jihar Kuros Riba ta na fama rashin samun kuɗi isassu daga Gwamnatin Tarayya da kuma tulin bashi."
"Mun amince da ƙarin kudin tallafin ne duba da yanayi ba wai son ranmu ba."

- Bassey Otu

Gwamna Otu ya ba ma'aikata hakuri

A bangaren biyan giratuti da sauran hakkokin ma'aikata, gwamnan ya roki al'umma da su yi hakuri inda ya ce yana kokarin shawo kan matsalar.

Gwamna Otu ya ba ma'aikata tabbacin ci gaba da kulawa da walwalarsu ba tare da matsala ba, cewar Daily Trust.

Ya bayyana babbar alaka da ke tsakanin gwamnati da ma'aikata inda ya ce sune sular ci gaban kowace Gwamnati.

Obaseki ya kara mafi karancin albashi N70,000

A wani labarin, Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiharsa.

Obaseki ya tabbatar da cewa zai fara biyan N70,000 a matsayin mafi karancin albashi a jihar duba da yanayin da ake ciki a kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading