Home Back

Minista Ya Kaddamar Aikin Titi Mai Tsawon Kilomita 1000 Daga Sakkwato, Kebbi Zuwa Legas

leadership.ng 3 days ago
Minista Ya Kaddamar Aikin Titi Mai Tsawon Kilomita 1000 Daga Sakkwato, Kebbi Zuwa Legas 

Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya kaddamar da babban titin Sokoto-Badagary mai tsawon kilomita 258 a Jihar Kebbi mai nisan kilomita 120.

Da yake kaddamar da ayyukan titunan a ranar Laraba a Birnin Kebbi, ministan ya ce idan aka kammala ayyukan zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Ya ce za a shinfida titin mai tsawon kilomita 915, haka kuma titin zai kawo abubuwan more rayuwa, yayin da zai fassara zuwa ingantaccen ƙira, rage cunkoson ababen hawa da haɓaka aminci tsakanin jihohi da ma kasashen Afirka.

Sanata Umahi, ya bayyana cewa aikin shimfida titin zai ba da damar hada fasahohin zamani, da inganta tsarin sufuri mai inganci da dorewar kasuwanci a tsakanin jihohi da kasashen Afirka.

Minista

Ministan, ya ci gaba da bayyana cewa, ayyukan da aka tsara za su kaucewa matsalolin da lalacewar kalubalen hanyoyi da jama’ar kasar nan ke fuskanta.

Haka kuma za a dauki tsawon lokaci kafin fuskanta matsalar gyaran hanyoyin da ake fama da su a shekarun baya, yayin da hanyar za ta ratsa jihohi bakwai da suka hada da; Jihar Kebbi mai fadin titin kilomita 258.

Ya kara da cewa za a yi ta ne ta hanyar Katami, Dabai, Gudale, Jabaka, Argungu, Ambursa, Gwandu, Tambuwal, Kambaza, Aliero, Jega, Maiyema, Karaye, Suru Asarara da Kwaifa.

Sauran sun hada da; Kalgo, Dakingari, Zagga, Bagudo, Gendini, Yamusa, Kwasara, Bahindi, Gwamba, Ka’oje da Buya, inda ya ce hakan zai hada da kara kaimi zuwa Birnin Kebbi.

Minista Umahi, ya yaba wa kokarin gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris bisa jajircewarsa na ganin an samu ci gaba cikin sauri a jihar.

“Na gamsu da ayyukan raya kasa na wannan gwamnati, nan ba da dadewa ba Jihar Kebbi za ta yi gogayya da Amurka, kan samun ayyukan masu amfani ga jama’ar jihar,” in ji shi.

Minista

A nasa jawabin gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya gode wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kan ajandar sabunta begensa, inda ya kara da cewa ajandar na da tasiri kai-tsaye ga rayuwar talakawan kasar nan.

Ya yaba da kokarin Ministocin Ayyuka, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Tattalin Arziki da karamin Ministan Ilimi da kuma ‘yan Majalisar Dokoki ta Kasa (Sanatoci da Wakilai) bisa gagarumin goyon bayan da suke bayarwa wajen cimma manufofin da aka ambata.

“Mun gamsu da manufa da hangen nesa na Shugaban kasa kan ‘Renewed Hope Agenda’, shiri ne da ya taba rayuwar ‘yan Nijeriya, muna biyayya ga APC daga sama har kasa,” in ji shi.

Minista

Wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron sun hada da; Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, Sanata mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Sanata Muhammadu Adamu Aliero, tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Sa’idu Usman Dakingari, Shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa, Shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar dokokin na tarayya, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da sauransu.

People are also reading