Home Back

Dalilin Tashin Farashin Wake A Nijeriya

leadership.ng 4 days ago
Za A Zuba Dala Miliyan 520 Don Habaka Noma A Jihohin Kudancin Nijeriya

Tsadar farashin Wake, ya jefa fargaba a zukatan mutane da dama a Nijeriya; wanda har yanzu ke ci gaba da haifar da cece-kuce.

An ruwaito cewa, tashin farashin Waken na kokarin wuce gona da iri, wanda a tarihi ba a taba ganin irinsa a fadin wannan kasa ba.

Har ila yau, manoman sun danganta wannan tsada tasa a kan abubuwa da dama da suka shafi nomansa a Nijeriya.

Kungiyar Manoman Farin Wake ta Kasa (CFAN), ta sanar da cewa; ana daukar mataki don lalubo mafita a kan wannan hauhawar farashi a fadin wannan kasa.

Shugaban kungiyar na kasa reshen Jihar Kano, Malam Sale Maigari Tunfafi ya sanar da cewa, ba Wake kadai wannan hauhawar farashi ya shafa ba, sai dai kawai tashin farashin Waken ne ya fi munana.

Ya sanar da cewa, daya daga cikin abin da ya jawo tsadar shi ne; raguwar da aka samu ta masu yin nomansa a bara, inda ya yi nuni da cewa, Wake na daya daga cikin amfanin gona da ake girbewa a duk shekara.

Ya kara da cewa, kutsawar da Fulani Makiyaya ke yi cikin gonakin da aka yi shuka, na haifar da lalacewar amfanin da aka shuka.

Kazalika, ya danganta hauhawar farashin kayan nomansa; wanda ya jawo aka samu raguwar yawan masu yin nomansa a fadin wannan kasa.

Ya ci gaba da cewa, shigo da Waken da wasu manyan dillalansa ke yi daga makwabtan kasashen Nijieriya, ya kara haifar da wannan hauhawar farashi nasa a wannan kasa.

A cewarsa, fadauwar darajar Naira; ita ma ta taimaka wajen haifar da tashin farashin nasa, wanda hakan ya sa wasu manyan dillalansa ke fitar da shi zuwa wasu kasashe, domin samun kudin musaya da kuma kazamar riba.

Ya bayyana cewa, tuni sun fara daukar matakai; domin noma Waken da yawa, wanda hakan zai sa tsadar tasa ta ragu.

Rahotannin sun yi nuni da cewa, farashin nasa ya haura Naira 200,000 duk loka daya, wanda ake ganin shi ne mafi munin tashin farashinsa a shekaru da dama da suka gabata.

People are also reading