Home Back

Abin da ya sa muke farautar Yahaya Bello – Shugaban EFCC

premiumtimesng.com 2024/5/19
Abin da ya sa muke farautar Yahaya Bello – Shugaban EFCC

Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya yi ƙarin haske dangane da farautar tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello da suke yi, da kuma irin zargin satar maƙudan biliyoyin nairorin da ake yi wa tsohon gwamnan.

A ranar Talata ce Shugaban EFCC ya yi wannan ƙarin haske, bayan wasu caje-caje 19 da aka gabatar a kan sa a kotu, wadda ya arce ya ƙi bayyana gaban kotun, lamarin da ya kai ana farautar sa

A Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja dai ana zargin sa da karkatar da fiye da Naira biliyan 80.

Shugaban EFCC ya bayyana cewa daga ciki Naira biliyan 80 da ake nema hannun Yahaya Bello, ya kamfaci Dalar Amurka daga kuɗin Jihar Kogi, ya biya kuɗin makarantar wani ɗan sa ɗaya.

Haka Olukoyede ya bayyana a Abuja, a ranar Talata, lokacin da yake magana a wani taron manema labarai.

Wannan bayani dai gidan talbijin na Channels ta nuno Olukoyede ɗin ya na yin wannan iƙirari kan Yahaya Bello, a shafin ta na Facebook.

Ya ce wani jami’in kuɗaɗe na Gidan Gwamnatin Jihar Kogi ne a Lokoja ya biya kuɗaɗen daga aljihun gwamnatin jiha.

EFCC ta ce an biya kuɗaɗen ta hannun wani ɗan canji, amma Olukoyede bai ambaci sunan ɗan canjin ba.

“Ta yaya haka kawai saboda gwamna ya san zai sauka daga mulki, sai ya kamfaci kuɗaɗen gwamnati, ya biya kuɗin makarantar ɗan sa na tsawon lokaci nan gaba har Dala 720,000.

“A matsiyaciyar jiha kamar Kogi fa aka yi wannan badaƙala, kuma ka na so na rufe ido na don kada a ce wai ana amfani da ni? To wa ke amfani da ni a waɗannan shekaru da na yi a duniya?”

A cikin bidiyon na tsawon mintina 3 da sakan 27, Olukoyede ya yi kira ga ‘yan Najeriya su garzaya kotu da kwafe-kwafen hujjojin yadda Yahaya Bello ya karkatar da Naira biliyan 80.

A ranar Talata ce kuma Babbar Kotun Tarayya ta umarci EFCC su kai wa lauyan Bello sammacin bayyana a kotu

ASHAFA MURNAI

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar EFCC ta aika wa tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello sammacin neman Naira biliyan 80 a wurin sa ta hannun lauyan sa.

A wani umarni da Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar a ranar Laraba, ya ce EFCC ta aika da sammacin ganin yadda Bello wanda ya ari takalmin kare ya falfala a guje, bai hallara a kotun ba, a ranar Talata ɗin.

Wannan ne karo na biyu da Yahaya Bello ya ƙi halartar zaman kotun da aka gayyace shi, domin EFCC ta gurfanar da shi.

Rashi halartar sa kotu ne ya kawo tsaikon shari’ar a ranar 18 ga Afrilu.

Tun a ranar 17 ga Afrilu ne dai kotu ta bada sammacin kamo Bello domin EFCC ta gabatar da shi a washegari 18 ga Afrilu, amma ‘yan sandan da ke gadin gidan sa a Abuja suka yi artabu da jami’an EFCC, har Gwamnan Kogi, Ododo wanda ya gaji Bello ya fice da shi a cikin motar sa.

Daga nan ne hukumomin gwamnatin tarayya su ka bayyana neman Yahaya Bello ruwa a jallo.

An dai yi artabu a gidan Yahaya Bello da ke Zone 4, Abuja.

A yau Talata sai Mai Shari’a ya umarci lauyan EFCC, Kemi Pinheiro ya aika sammacin neman Yahaya Bello ga lauyan sa, Abdulwahab Mohammed.

Nwete ya ce ya yi amfani da Doka ta Sashe na 382(4) da (5).

Bello Ya Nemi A Soke Neman Sa Ruwa Jallo Da Ake Yi:

Sai dai kuma jim kaɗan bayan kotu ta ce lauyan EFCC ya aika wa lauyan Yahaya Bello sammacin shi Bello ɗin, sai wani lauya ya miƙe a madadin Yahaya Bello ya nemi kotu ta soke farautar tsohon gwamnan da jami’an tsaro ke yi.

Lauyan mai suna Adeola Adedipe (SAN), ya ce a soke sammacin farauta Yahaya Bello, saboda mai shari’a ne da kan sa ya bayar da sammacin, ba wani ɓangare ne na masu shigar da ƙara suka nemi a bayyana sammacin farautar Bello ɗin ba.

People are also reading