Home Back

Ana Rigimar Mafi Karancin Albashi, Naira Ta Fado a Kasuwa Bayan Dala Ta Sake Ƴunkurawa

legit.ng 2024/7/1
  • Darajar Naira ta fadi a kasuwannin Najeriya bayan samun habaka na wasu kwanaki yayin da dala ta tashi
  • A jiya Juma'a 7 ga watan Yuni an siyar da dala kan N1,483 sabanin N1,481 a ranar Alhamis 6 ga watan Yuni a kasuwanni
  • Rahoton FMDQ ya tabbatar da cewa hakan ya nuna darajar Naira ta fadi da 0.16% kenan wato N2.50 a jiya Juma'a 7 ga watan Yuni

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake ci gaba da hada-hadar ƴan canji a Najeriya, Naira ta yi ƙasa a kasuwa.

Darajar dala ta tashi a kasuwa bayan siyar da ita kan N1,483 a jiya Juma'a 7 ga watan Yuni.

Rahoton FMDQ ya tabbatar da cewa darajar Naira ta fadi da N2.50 idan aka kwatanta da ranar Alhamis 6 ga watan Yuni.

Wannan faduwa na darajar Naira ya nuna ta samu nakasu da 0.16% idan aka kwatanta da ranar Alhamis din makon da ya wuce.

A ranar Alhamis 6 ga watan Yuni an siyar da dala kan N1,481.49 sabanin jiya Juma'a da kasa siyar kan N1,483.99.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, yawan daloli da ke kasuwa ya karu daga $213.31m a ranar Lahadi zuwa $269.27m a jiya Juma'a 7 ga watan Yuni.

Karin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

People are also reading