Home Back

RUWAN DARE GAME DUNIYA: Ɗangote zai raba shinkafar Naira biliyan 13 ga marasa galihu a jihohi 36

premiumtimesng.com 2024/4/29
RUWAN DARE GAME DUNIYA: Ɗangote zai raba shinkafar Naira biliyan 13 ga marasa galihu a jihohi 36

Ƙasaitaccen attajirin da ya fi kowa ƙarfin arziki a Afrika, Aliko Ɗangote, ya ƙaddamar da gagarimin aikin jinƙai na raba shinkafa wadda kuɗin ta ya kai Naira biliyan 13 ga marasa galihu, a faɗin ƙasar nan.

Ɗangote zai raba shinkafar a ƙarƙashin Gidauniyar Ɗangote.

Haka kuma yanzu haka a kullum gidauniyar ta na raba abincin buɗe-baki ga mabuƙata 10,000 a Jihar Kano.

Cikin wata sanarwar da ɗaya daga cikin jami’an gidauniyar, mai suna Samira Sanusi ta fitar a Kano, ta ce Gidauniyar Ɗangote za ta raba buhunan shinkafa har miliyan 1 a faɗin ƙasar nan, cikin jihohi 36 da Yankin Abuja, domin rage wa marasa galihu raɗaɗin tsadar rayuwa.

Samira ta ce wannan tallafi ya na tafe ne bayan da kuma a kullum ana raba biredi sunƙi 20,000 a kullum a Kano sai kuma sunƙi 15,000 kullum a Legas, wanda gidauniyar ta fara a cikin 2020, lokacin zaman kullen korona.

Samira ta bayyana cewa abincin ciyarwar Ramadan da Ɗangote Foundation ke rabawa, akwai jalaf, shinkafa da miya, jalaf ɗin taliya, doya, wake da naman kaji da naman shanu, tare da robar ruwa da robar lemo ga duk mabuƙaci ɗaya.

Ta ce ana raba abincin a masallatan Juma’a, kan titina, gidajen kurkuku, gidajen marayu, gidajen kangararrun yara da wasu wurare a cikin Kano da kewaye.

Baya ga irin wannan ciyarwa da Gidauniyar Ɗangote ke yi tsawon shekaru huɗu kenan a jere, Ɗangote na ciyar da mabuƙata a ɓoye ba tare da sanar ba, har tsawon fiye da shekaru 30 kenan.

Ta ce ana yin wannan daɗaɗɗiyar ciyarwa a gidan mahaifiyar sa da ke unguwar Ƙoƙi, har ma da wasu wurare daban-daban.

A ƙarƙashin wannan, a kullum ana ciyar da mutum 10,000 abincin safe, na rana da na dare, fiye da shekaru 30 kenan ba a daina ba.” Cewar Samira.

 
People are also reading