Home Back

Barayi Sun Haura Gida Sun Yi Ta’asa, An Sacewa Bayin Allah Ragon Layya a Abuja

legit.ng 2024/7/6
  • Barayi sun haura gida sun sace ragon layya yayin da ake kuka kan tsadar raguna a kasuwannin Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a unguwar Sabon Tasha da ke birnin tarayya Abuja a ranar Asabar
  • Makwabcin wanda aka sacewa ragon, Abdullahi Ahmed ya bayyana yadda ɓarayin suka shiga gidan tsakar rana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Yayin da bikin sallah yake kara ƙaratowa barayi sun shiga har gida sun sace ragon layya a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa wanda aka yiwa satar ya fita daga gidan ne kafin barayin su shigo su aikata ta'asar.

Raguna
Barayi sun sace ragon layya a Abuja. Hoto: Legit Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa barayin sun shiga gidan mutumin ne tsakar rana suka sace ragon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace rago ana shirin layyah a Abuja

Wani makwabcin wanda aka sacewa ragon, Abdullahi Ahmed ya ce barayin sun shiga gidan ne da misalin karfe 1:12 na rana.

Bayan mai gidan ya dawo da misalin karfe 4:00 na yamma sai ya nemi ragon ya rasa, sai igiya kawai ya gani.

Nawa aka saye ragon sallar?

Makwabcin ya tabbatar da cewa an sayi ragon ne a kan kudi N215,000 a makon da ya wuce domin hidimar babbar salla.

Duk da cewa an tuntubi rundunar yan sandan birnin tarayya amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu amsa daga wajen su kan lamarin ba.

Ragon sallar layyah ya gagari talaka

A wani rahoton, kun ji cewa magidanta sun koka kan tsadar kayan masarufi yayin da hidimar bikin babbar sallah ke kara ƙaratowa a tarayyar Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun fifita sayan kayan abinci a kan sayan raguna domin gabatar da ibadar layya a wannar shekarar.

An ba malamai kyauta a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ba malaman addinin Musulunci gwaggwaɓar kyauta domin hidimar sallar layya.

Rahotanni sun nuna cewa kwamishinan harkokin addini na jihar Sokoto, Dakta Jabir Sani Mai Hula ne ya bayyana lamarin ga manema labarai.

Asali: Legit.ng

People are also reading