Home Back

Babbar Kotun Kano ta cire wa Ganduje waigin dakatarwar da aka yi masa a APC

premiumtimesng.com 2024/5/19
Lokaci bai ƙure wa Atiku da Obi ba, za su iya zama shugaban kasa bayan Tinubu ya kammala zangon biyu a 2031 – Ganduje

Ranar Litinin ce Mai Shari’a Usman Na’Abba na Babbar Kotun Kano, ya amince da roƙon da lauyan Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje ya yi, inda ya nemi a ɗage dakatarwar da kotun ta jaddada kan Ganduje.

Lauyan Ganduje ya nemi a cire dakatarwar, kuma kotu ta amince.

Mai Shari’a ya ce ɓangarorin biyu su tsaya matsayin da suke kafin ranar 15 ga Afrilu.

A ranar 17 ga Afrilu ce Mai Shari’a Na’Abba ya umarci Ganduje ya daina kiran kan sa shugaban APC.

To sai dai kuma a ranar Litinin lauyan Ganduje ya nausa kotu, ya nemi a soke dakatarwar, kuma Mai Shari’a ya amince.

To sai dai kuma wata sabuwar jangwangwama ta ɓalle, yayin da wani gungun shugabannin mazaɓa sun ƙara lafta wa Ganduje hukuncin ‘dakatarwa’ daga APC.

Wani gungun shugabannin APC da suka ɓalle daga mazaɓar Ganduje cikin Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, sun ayyana ƙara tafta wa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje kuma Shugaban APC na Ƙasa, takardar dakatarwa daga jam’iyya.

Wannan sabuwar dakatarwar dai ta fito ne daga wani gungun da ya kira kan sa halastattun shugabannin APC na ƙauyen Ganduje, sun ce sun dakatar da Ganduje bisa dalilai na zargin sa da yi wa jam’iyyar APC zagon-ƙasa, wato ‘anti-party’.

Haka dai wani mai suna Ja’afar Ganduje wanda ya yi wa manema labarai jawabi ya bayyana a ranar Lahadi.

Ja’afar ya ce ya na magana ne da yawun sauran shugabanni 11 na APC da ke ƙauyen Ganduje.

Ya ce an zargi Abdullahi Ganduje da yin zagon-ƙasa ga APC a zaɓen da ya wuce na 2023.

Ya kuma yi zargin cewa Abdullahi Ganduje ya ƙi biyan kuɗaɗen harajin da APC Reshen Mazaɓa ke karɓa a hannun mambobin ta daga sama har ƙasa.

Ya kuma zargi Abdullahi Ganduje da haddasa husumar da ta raba kan shugabancin APC a Mazaɓar Ganduje.

People are also reading