Home Back

Badakalar N84bn: Kotu Ta Amince da Bukatar Hukumar EFCC Na Cafke Yahaya Bello

legit.ng 2024/5/12

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta amince da bukatar hukumar yaki da yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC) na kama Yahaya Bello.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kotun ta baiwa EFCC izinin cafke tsohon gwamnan jihar na Kogi, a shirye-shiryen gurfanar da shi a ranar Alhamis, talabijin na Channels ya ruwaito.

Mai shari’a Emeka Nwite ya baiwa hukumar EFCC takardar izinin kamun nan take a yammacin yau Laraba, 17 ga watan Afrilu.

Wannan dai na zuwa ne bayan wata babbar kotun jihar Kogi ta yanke hukuncin hana EFCC kama tsohon gwamnan ko tsare shi ko kuma gurfanar da shi gaban kuliya.

Cikakkun bayanai na zuwa daga baya…

Asali: Legit.ng

People are also reading