Home Back

InnalilLahi: Wata Hajiya Daga Najeriya Ta Yi Ajalin Kanta a Madina, Saudiyya Ta Yi Martani

legit.ng 2024/7/7
  • Yayin da ake yawan samun mace-mace a Saudiyya, wata Hajiya daga jihar Kwara Najeriya ta riga mu gidan gaskiya
  • Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da cewa matar mai suna Hajiya Hawawu ta rasu ne bayan yin ajalin kanta
  • Wannan na zuwa ne bayan rasuwar wani Alhaji daga jihar mai suna Saliu Mohammed bayan gamuwa da rashin kafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Madina, Saudiyya - Ana zargin wata Hajiya mai suna Hawawu ta hallaka kanta a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.

Hajiyar ta fito ne daga jihar Kwara inda hukumomin Saudiyya suka tabbatar da haka bayan gudanar da bincike.

Hukumomin sun sanar da hukumar alhazai ta jihar Kwara yadda al'amarin ya faru a Madina bayan samun gawar matar, cewar Tribune.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren hukumar, Abdulsalam AbdulKabir ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce hukumomin Saudiyya sun gudanar da bincike inda suka tabbatarvda cewa ta yi ajalin kanta ne a saman dakinta da ke Madina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar wani mahajjaci daga jihar Kwara mai suna Saliu Mohammed wanda ya rasu bayan faduwa rashin lafiya.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading