Home Back

Sarautar Kano: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Tauye Hakkin Aminu Ado, Ta Ci Tarar Abba Kabir N10m

legit.ng 2024/10/5
  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, Babbar Kotun Tarayya ta ci tarar gwamnatin jihar N10m
  • Kotun ta dauki matakin ne bayan umarnin gwamnan jihar, Abba Kabir na cafke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero
  • Babbar kotun ta ce umarnin gwamnan ya sabawa sashe na 35(1) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 na ƴancin ɗan Adam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano ta ci tarar gwamnatin jihar N10m kan rigimar sarauta.

Kotun ta dauki wannan matakin ne bayan gwamnatin jihar ta ba da umarnin cafke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Hakan, a cewar kotun ya saba dokar ƴancin ɗan Adam na yawo da zirga-zirga kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar, cewar Justice Watch News.

Hakan ya biyo bayan umarni daga gwamnatin jihar na cafke Aminu Ado kan zargin neman ta da zauna tsaye a jihar.

Kotun ta ce umarnin cafke Aminu Ado ya saba sashe na 35(1) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce matakin ya take masa hakkin zirga-zirga da kuma tilasta killace shi a gida sabanin sauran ƴan kasa saboda umarnin cafke shi da aka bayar.

Daga bisani kotun ta bukaci gwamnatin jihar ta biya Aminu Ado diyyar N10m saboda take masa hakkinsa na ɗan kasa.

Kotun ta kuma dakatar da kamawa ko barazana da cin mutunci ko kuma tsare Aminu Ado Bayero domin kare masa ƴancinsa na ɗan Adam.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading