Home Back

Mafi Karancin Albashi: Akwai Yiwuwar Kungiyar NLC ta Amshi Tayin Gwamnati

legit.ng 2024/7/1
  • Rahotanni sun fara bayyana cewa akwai yiwuwar gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago su cimma matsaya kan batun albashi da ya dade yana yamutsa hazo
  • Wasu majiyoyi sun bayyana cewa akwai kwararan alamu dake nuna cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) za ta iya amicewa da tayin N100,000 a matsayin albashin
  • Tun bayan kungiyoyin sun bayyana bukatarsu ta neman gwamnati ta N494,000 a matsayin albashin 'yan kasar nan masu ruwa da tsaki ke ganin nauyin ya yiwa Najeriya yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Alamu sun fara karkata kan cewa kungiyar kwadagon kasar nan (NLC) da takwarorinta dake fafutukar a samawa ma'aikatan kasar nan mafi karancin albashi su amshi tayin gwamnati.

Bayanai na nuna cewa kila kungiyoyin kwadagon ku karbi tayin N100,000 da ake ganin kwamitin mafi karancin albashin gwamnatin tarayya zai yi musu.

Nigeria Labour Congress HQ
Mafi karancin albashi: NLC da gwamnati za su iya tirkewa kan N100,000 Hoto: Nigeria Labour Congress HQ Asali: Facebook

Punch News ta jiyo daga wasu majiyoyi cewa 'yan kungiyoyin kwadago sun janye yajin aikin da suke yi domin ba su damar ci gaba da tattaunawa da gwamnati na tsawon kwanaki biyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC na sake duba bukatarta na N494,000

Naija News ta wallafa cewa kungiyoyin kwadago sun fara sake shawara tare da kokarin rage N494,000 da suka nemi gwamnati ta biya tun da fari zuwa N100,000.

Masu ruwa da tsaki da dama, ciki har da shugaban majalisa Godswill Akpabio sun bayyana cewa bukatar biyan N494,000 a matsayin mafi karancin albashi zai yi wahala.

A sanarwa da ya fitar ranar Asabar, shi ma Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana cewa idan har aka amince da bukatar NLC, za a kashe N9.5tn duk shekarar.

Ya ce nauyin zai yiwa kasar nan yawa kuma ba za ta iya daukarsa ba a halin da ake ciki.

NLC: An fadi mafi karancin albashi

A wani labarin kun ji cewa kungiyar 'yan kasuwa ta TUC ta janye yajin aikin sai baba-ta-gani da ta tsunduma, tare da fadin kudin da take ganin zai fi dacewa da ma'aikata.

Shugaban kungiyar, Festus Osifo ya bayyana cewa ba za su amince da N60,000 da gwamnati ta yi musu tayi ba, amma kamata ya yi gwamnati ta yi tayi mai gwabi.

Asali: Legit.ng

People are also reading