Home Back

Gwamnatin Yobe Ta Fadi Amfanin Tubabbun 'Yan Boko Haram Cikin Al'umma

legit.ng 2024/7/1
  • Gwamnatin jihar Yobe ta kare matakinta na yin amfani da tubabbun ƴan Boko Haram wajen samar da tsaro a jihar
  • Gwamnatin ta bayyana cewa tubabbun ƴan Boko Haram ɗin na taimakawa wajen yaƙi da ta'addanci da samar da tsaro a jihar
  • Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro wanda ya bayyana hakan ya ce suna taimakawa wajen samo bayanai kan ƴan ta'addan Boko Haran da ISWAP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa tubabbun ƴan Boko Haram na taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci a jihar.

Gwamnatin ta ce tubabbun ƴan Boko Haram ɗin na taka rawar gani wajen kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'adda.

Gwamnatin Yobe ta fadi amfanin tubabbun Boko Haram
Gwamnatin Yobe tubabbun 'yan Boko Haram na taimkawa wajen yaki da ta'addanci Hoto: Mai Mala Buni Asali: Twitter

Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam, mai ritaya, mai ba Gwamna Mai Mala Buni shawara kan harkokin tsaro ne ya bayyana hakan, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Damaturu, rahoton Daily Post.

Menene amfani tubabbun Boko Haram?

Dahiru Abdulsalam yana magane kan damuwar da mutane suka nuna dangane da shigar tubabbun masu tayar da ƙayar bayan a ayyukan tsaro a garin Geidam.

"Babu wata gwamnati da za ta ɗauki duk wani matakin da zai cutar da al'ummarta. Gwamnati ta himmatu wajen kawo ƙarshen tada ƙayar baya domin mu samu zaman lafiya."
"Muna da waɗannan tubabbun ƴan Boko Haram da ake kira ‘hybrid Force’ da ke taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyuka a Damaturu, Goniri da Buni Yadi."
"Na farko, suna taimakawa wajen samun bayanai game da ƴan ta'adda, ta hanyar majiyoyinsu da ke cikin Boko Haram da ISWAP.
"Na biyu, suna taimakawa wajen samun bayanai game da abokan hulɗar Boko Haram da ISWAP da kuma masu yi musi safarar kaya."

- Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam

Jami’in ya ce an tura tubabbun ƴan Boko Haram zuwa Geidam ne domin su taimaka wajen daƙile kwararowar ƴan ta’adda da abokan hulɗarsu zuwa cikin garin

Gwamnan Yobe ya naɗa Sarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya naɗa babban ɗan marigayi Sarkin Tiƙau, Abubakar Muhammadu Ibn Grema a matsayin sabon sarkin masarautar.

Gwamna Buni ya naɗa sabon Sarkin Tikau ne biyo bayan rasuwar Mai Martaba Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

People are also reading