Home Back

An Samu Hayaniya Bayan Sanatoci Sun Kaure da Faɗa a Majalisa da Aka Sabunta, an Fadi Dalili

legit.ng 2024/5/19

An samu hayaniya a Majalisar Dattawa bayan dawowa daga hutu a tsakanin Ssanatoci kan wurin zama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An kaure a Majalisar Tarayya kan wurin zama bayan sabunta dakin Majalisar a Abuja.

Lamarin ya faru a yau Talata 30 ga watan Afrilu bayan dawowa zaman Majalisar da aka shafe tsawon shekaru biyu ana gyara.

Sanata Danjuma Goje mai wakiltar Gombe ta Tsakiya da Sahabi Yau da ke wakiltar Zamfara ta Arewa sun nuna damuwa kan tsarin wurin zaman.

Sanatocin sun yi korafi ga Opeyemi Bamidele wanda shi ne shugaban masu rinjaye a Majalisar, cewar Punch.

Kamar yadda dokokin Majalisar suka nuna, Sanatoci suna zama ne a tsare bisa girman sanata a Majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun fito...

Asali: Legit.ng

People are also reading