Babban Jigon APC Ya Aike da Saƙo Ga Ƴan Majalisar Tarayya 60 da Ke Shirin Sauya Sheƙa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jigon jam'iyyar APC, Eze Chukwuemeka Eze, ya yi kira ga fusatattun ƴan majalisar tarayya 60 na PDP da su sauya tunani, ka da su sauya sheƙa daga jam'iyyarsu.
Idan baku manta ba Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa mambobin majalisar wakilan tarayya 60 sun yi barazanar ficewa daga jam'iyyar PDP.
Ƴan majalisar sun buƙaci muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum, ya yi murabus ko kuma sun sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyun, Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai da yake martani kan haka, jigon APC Mista Eze ya buƙaci dukkan masu kishin ƙasa su taimakawa ƴan majalisar su tsaya a PDP.
Mista Eze ya bayyana haka ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Patakwal, babban birnin jihar Ribas, kamar yadda Leadership ta tattaro.
Jigon jam’iyyar APC ya ce ‘yan majalisar dokokin jam’iyyar adawa, sun cancanci yabo saboda yunƙurin da suka yi na kubutar da jam’iyyar daga ƴan zagon ƙasa.
Ya zargi Damagum da hada baki da jiga-jigan makiya. PDP da gangan don gurgunta kokarin da ake yi na tabbatar da shugabanci a dukkan matakan jam'iyyar.
Eze ya nuna mamakinsa kan yadda muƙaddashin shugaban PDP ya bari mutuncinsa ya zube da kuma shiga cikin waɗanda ke ƙulla makirci lalata tsagin adawa.
Dangane da zargin cin hancin $30,000 da ministan Abuja ya ɗora wa shugabannin PDP, babban ɗan siyasar ya buƙaci hukumomin da abun ya shafa su gudanar da bincike mai zurfi.
Kuna da labarin cewa tsohon mataimakin shugaban APC ya buƙaci Bola Tinubu ya sulhunta Kwankwaso da Ganduje domin warware rikicin siyasar Kano.
Salihu Lukman ya ce wannan dama ce ga Tinubu da manyan jiga-jigan APC da za su jawo Kwankwaso kuma su ceto siyasar Ganduje.
Asali: Legit.ng