Home Back

Kano: Dalilai 3 da Za Su Hana Aminu Ado Bayero Kwace Sarauta Daga Hannun Sanusi II

legit.ng 3 days ago

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi da sarki na 15, Aminu Ado Bayero kowane daga cikinsu na ganin shi ne halastaccen sarkin Kano.

Tun watan Mayu bayan Gwamna Abba Kabir ya mayar da shi, Sanusi II ya kama aiki a babbar fada da ke Ƙofar Kudu yayin da Aminu Ado ya zauna a ƙaramar fadar Nassarawa.

Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Dalilan da suka sa zai wahala Aminu Bayero ya samu nasara kan Muhammadu Sanusi II Hoto: @Masarautarkano Asali: Facebook

Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta soke maido da Sanusi da sauran matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka kan sabunta dokar masarauta a majalisa.

Sai dai duk da wannan hukunci na kotu, Gwamna Abba ya kafe cewa Muhammadu Sanusi II ne sahihin sarkin Kano.

A wannan rahoton, Legit.ng ta yi duba kan abin da ke faruwa kuma ta tattaro maku dalilan da zai sa da wahala Aminu ya iya ƙwato sarauta daga hannun Sanusi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ƙarfin ikon gwamnatin jiha

A doka, naɗa sarakuna alhaki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin jiha kuma a wannan taƙaddama, gwamnatin Kano tana goyon bayan Sanusi II.

Legit Hausa ta gano cewa manyan kotunan tarayya ba su da hurumin tsoma baki a harkokin da suka shafi sarauta.

Doka ta ɗora nauyin kula da harkokin sarakuna kan gwamnatocin jihohi ne domin a taka ma duk basaraken da ya nemi wuce gona da iri.

2. Tasirin gwamnoni kan sarakunan gargajiya

A cikin shekaru sama da 20 da suka gabata, ƙarfin iko da tasirin sarakunan gargajiya ta dusashe idan aka kwatanta da kafin samun ƴancin kai da bayan ƴanci da ƴan shekaru.

Juyin mulki na farko da aka yi a 1966 shi ne tangarɗa ta farko da sarakuna suka samu, tasirinsu ya. fara raguwa.

Sauya fasalin ƙananan hukumomin da aka yi a 1976 ya ƙara kawo cikas ga sarakuna a Najeriya, inda ya tuɓe masu karfin da suke dogaro da shi a kundin tsarin mulki.

Lokacin da aka yiwa kundin tsarin mulki garambawul a 1999, babu wata doka da aka ware kan sarakuna amma a ƴan shekarun nan an yi ta kira-kirayen ya kamata su samu kariyar doka.

A 2019, sarakuna sun yi yunƙuri domin a maƙala su a kundin tsarin mulki, inda suka kafa wani kwamitin haɗin guiwa wanda ya mika buƙatarsu ga majalisar tarayya.

Sai dai har yanzun sarakuna na karkashin dokokin sarauta da gwamnatocin jihohi suka zartar, wannan ya sa gwamnoni ke yadda suka ga dama wajen naɗa sarakuna ko ma tsige su.

3. Tinubu ba zai biyewa Ganduje ba

Sanin kowane Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje makusantan juna ne a siyasa kafin saɓani ya raba su a shekarun da suka gabata.

Duk da Aminu Ado Bayero na taƙamar Ganduje, tsohon gwamna kuma shugaban APC na tare da shi, da yiwuwar Bola Ahmed Tinubu ba zai yarda ya goyi bayan Ganduje ba.

Ga dukkan alamu shugaban ƙasa ba zai tsoma baki a taƙaddamar sarautar Kano ba saboda kar hakan ya taɓa masa siyasarsa.

Gwamna Abba ya soki fadar Nassarawa

A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilin da ya sa aka ga tuta a ƙaramar fadar Nassarawa, wurin da Aminu Ado Bayero ke zaune

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tona ya ce fadar ta ɗaga tutar ne domin jawo hankalin jama'a

Asali: Legit.ng

People are also reading