Home Back

Me zuwan kwararrun sojin Rasha jamhuriyar Nijar ke nufi?

bbc.com 2024/5/16
Putin da Tchiani

A ranar Laraba ne, ƙwararrun sojoji daga Rasha suka isa jamhuriyar Nijar domin horas da sojojin ƙasar.

Hakan na zuwa ne bayan da Nijar ɗin ta umarci sojojin Amurka da Faransa su fice daga ƙasar bayan da sojoji suka kwace mulki a shekarar da ta gabata.

Sojojin sun isa Nijar tare da wasu na'urori da za su yi amfani da su wajen kafa garkwuwar kariya daga hare-hare ta sama, wadda ke iya hana duk wani abu da ba a yarda da shi ba ratsawa ta sararin samaniyar ƙasar.

Za su kuma bai wa sojojin ƙasar horo yadda za su yi amfani da su.

Nijar ta soke daɗaɗɗiyar alaƙar diflomasiyya da tsaro da Faransa kuma kamar Mali da Burkina Faso, tana kusanta kanta ga Rasha domin samun tallafi wajen yaƙar masu iƙirarin jihadi.

Zuwansu sojojin Rasha Nijar, ya nuna yadda Moscow ke ci gaba da ƙarfafa tasirinta a yankin Sahel na yammacin Afirka da ke fama da rikici.

Shin ya masana ke kallon wannan mataki?

Masani kan harkar tsaro a yankin Sahel, Abdulrahman Alkasim ya ce wannan ba shi ne karon farko ba da sojojin Rasha ke zuwa Nijar, sai dai zun zo ne a daidai lokacin da Nijar ɗin ke ce-ce-ku-ce tsakaninta da sauran ƙasahen yamma.

"Su ƙasashen Yamma suna so su samu gindin zama ita ma Rasha abin da take nema kenan. Da zuwan sojojin Rasha sun bayyana cewa sun zo da kayan aiki da dakaru don horas da sojin Nijar," in ji Alkasim.

Ya ce a baya suna zuwa horaswa amma ba a bayyanawa sai a wannan lokaci.

Masanin ya ce sojojin sun bayyana cewa su sojin ƙasar Rasha ne ba na Wagner ba, wanda yanzu babu ita ƙungiyar.

"Abin da suka zo da shi ana iya cewa zai taimaka ganin irin takun tsaka da Nijar ke yi da wasu ƙasashen Yamma, kuma hakan zai taimaka game da barazanar kai mata hari da kuma na 'yan ta'adda," in ji shi.

Ya ce ko da akwai wannan barazanar, amma akwai alamu an kusa shawo kanta ko kuma a ce kaɗan ta rage.

Yaya alaƙar Nijar da tsoffin iyayen gidanta za ta kasance?

Masani Abdulrahman Alkasim ya ce za a iya cewa alaƙar Nijar da Faransa tuni ta zama tarihi bayan janye wakilicin jakadancinsu, kuma babu wani wakilci tsakaninsu.

"Yanzu abin da za a jira a gani shi ne ita ma Amurka sojojin mulkin Nijar ɗin sun kayyaɗe musu lokacin ficewa faga ƙasar saboda wadda ake da ita ba ta girma ka'idar ƙasa da ƙasa ba. Zuwan sojojin Rasha yanzu ya ƙara nuna cewa zamansu ba zai yu ba," in ji Alkasim.

Masanin ya kuma ce kawo na'urorin hangen nesa da aka kawo Nijar ɗin na nuwa cewa babu shirin kawo mata hari da ba za ta gani ba yanzu.

Nijar dai ta soke yarjejeniyar soji da Amurka a watan ya gabata, kuma hakan na zuwa ne 'yan watanni bayan da hukumomin sojin ƙasar suka yanke irin wannan alaƙa da Faransa, inda har ma aka kori dakarun tsohuwar uwar gijiyar tata ta mulkin mallaka da ke yakar masu ikirarin jihadi a yankin daga ƙasar.

Sai dai, bayanai sun ce har yanzu rundunar sojin Amurka na ci gaba da tattaunawa da gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin domin ta amince sojojinta da kuma ma'aikatanta farar hula su riƙa shiga ƙasar

Masana dai na nuna mamaki dangane da yadda sojojin jamhuriyar ta Nijar suke sassauya al'amuransu kasancewar a farkon juyin mulkin ƙasashen Amurka da Togo ne masu shiga tsakani.

'Yankin Sahel ya koma wuri da ƙasashen yamma da na Gabas ke rububin zuwa'

Masani Abdulrahman Alkasim ya ce wannan ba karon farko bane da sojojin Rasha ko na wasu ƙasashen Gabas Ta Tsakiya ke zuwa Nijar domin horaswa da sojin ƙasar.

Ya ce akwai jiragen yaƙi sumfurin SU21 da kuma mai saukar ungulu na M18 da M20 waɗanda Rasha ta ƙera, inda sojin ƙasar da na Ukraine suka zo suka horas da sojojin Nijar kuma suke amfani da su.

"Hakan ya faru ne a 2007 lokacin mulkin shugaba Tanja Mamadou. Amma na yanzu ya zo ne lokacin da Nijar ke ce-ce-ku-ce da ƙasashen Yamma kuma a lokaci na yaƙin Ukraine wadda Rasha ke kai hari da kuma na Gaza," in ji shi.

Ya ce yankin Sahel ta dawo yanki da ƙasashen yamma da na Gabas ke ƙoƙarin samun iko saboda irin albarkatu da yankin ke da shi kamar Uranium, Zinare, da kuma karafa da ake nema don yin bincike.

Me ƴan Nijar ke cewa?

Ƴan Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Masanin ya ce akwai ƴan Nijar da ke goyon baya da kuma waɗanda ba sa maraba da zuwan sojin na ƙasar Rasha.

"Da ma a Nijar akwai sojojin ƙasashe da dama waɗanda ƙasar ke alaƙa da su da ke zuwa suna horas da sojoji ko kuma waɗanda take sayen makamaki a wurinsu," in ji shi.

Ya ce akasarin al'ummar Nijar na son ganin sabon tsari na alaƙa da wasu ƙasashe wanda suke ganin shi zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da ƙasar ke fama da shi.

Matsalar tsaro dai na ƙaruwa a ƙasar tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli, wanda ya hamɓarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum.

Sai dai sojojin sun ce dalilai na rashin tsaro ne suka sa su yin juyin mulki.

Rahotanni na nuna cewa masu tayar da ƙayar baya na ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar, musamman a yankin Tilaberi.

People are also reading