Home Back

SHIRIN INGANTA KARATUN FIRAMARE: Gwamnatin Kano za ta kashe Naira biliyan 4.8 wajen inganta makarantun jihar

premiumtimesng.com 3 days ago
DAGA GIDA-GIDA ZUWA GIDAN GWAMNATI: Wane Ne Abba Gida-gida?

Gwamnatin Jihar Kano ta amince a kashe Naira biliyan 4.8, wajen gyaran makarantu, gina sabbin ajujuwa da kuma ɗaukar masu kula da tsaron makarantu a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Wannan ya na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai Sanusi Bature ya fitar, a ranar Talata.

Ya ce Gwamna Abba Kabir-Yusuf ya amince da haka a wurin taron Majalisar Zartaswa ta Jihar Kano, na 15.

“Ina farin cikin sanar da ku cewar mun fitar da kuɗi naira biliyan 1 da miliyan 903 da dubu 315 da ɗari 617 ga ƙananan hukumomi 44 da ke nan Jihar Kano domin gyaran ajujuwan makarantu a faɗin Jihar Kano ta hannun Kwamitin CRC, ƙarƙashin kulawar Hukumar Ilimin bai ɗaya ta SUBEB.

“Bugu da ƙari, na kuma amincewa da fitar da kuɗi Naira biliyan 2 da miliyan 925 da dubu 140 da ɗari 591 da kobo 60, domin gina sabbin ajujuwa a faɗin Jihar Kano. Wannan kashi na farko ne na yunƙurin gina sabbin ajujuwa da suka dace da yanayin koyo da koyarwa a faɗin Jihar Kano.

“Wannan kuɗaɗe da muka fitar wani ɓangare ne na ayyana dokar ta-baci kan ilimi a Jihar Kano, don haka za mu ci gaba da fitar da ƙarin kuɗaɗen nan gaba kaɗan domin ganin mun magance dukkanin matsalolin da suka shafi ilimi a jihar Kano.” Inji Gwamna Abba.

Ya ce kuma za a ɗauki masu gadin makarantu mutum 17,000, wato mutum 400 a kowace ƙaramar hukuma, daga ƙananan hukumomin Jihar Kano 44, domin su riƙa kula da daba kariya ga makarantun.

People are also reading