Bola Tinubu Na Jagorantar Taron FEC a Fadar Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito
FCT Abuja - Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) yanzu haka a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Taron na gudana ne a ɗakin taron majalisar da ke fadar gwamnatin Najeriya yau Talata, 25 ga watan Yuni, 2024.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, taron FEC na yau na zuwa ne bayan wanda aka yi kwana biyu ana yi kusan makonni shida da suka gabata.
A zaman FEC na ƙarshe. gwamnatin Bola Tinubu ta amince da ayyuka daban-daban har guda 20.
Waɗanda suka halarci taron da ke gudana yanzu haka sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati Femi Gbajabiamila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bugu da ƙari, an tattaro cewa mafi akasarin ministocin Bola Tinubu sun halarci taron FEC a wannan karon.
Idan zaku iya tunawa Shugaba Tinubu ya kaddamar da majalisar ne ranar 28 ga watan Augusta, 2023 kuma ya sauya ranakun taron daga Laraba zuwa Litinin a kowane mako.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris, a ranar 16 ga Oktoba, 2023, ya bayyana cewa majalisar za ta rika zama ne idan akwai muhimman batutuwan da za a duba.
"Saboda haka daga yanzu taron FEC ya koma ranakun Laraba kuma ba lallai ne kowane mako za a yi taron ba, idan babu batun da za a tattauna, z a ɗaga zuwa mako na gaba."
Asali: Legit.ng