Gwamna Ya Dakatar da Babban Hadiminsa, Ya Umarci Ya Bar Ofis Nan Take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osogbo, jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke ya dakatar da Emmanuel Adebisi, babban mai taimaka masa na musamman kan harkokun kungiyoyin fararen hula.
Mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 3, ga watan Yuli, 2024.
Gwamna Adeleke ya bayar da umarnin dakatar da hadimin nan tkae babu ba ta lokaci, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai gwamnan bai bayyana asalin dailin da ya jawo ya ɗauki matakin dakatarwa kan Mista Emmanuel Adebisi ba.
Sanarwar ta ce:
"Gwamna Adeleke ya dakatar da Emmanuel Adebisi nan take har sai na gama binciken da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jiha, Kazeem Akinleye zai jagoranta."
Bayan haka gwamnan ya gargaɗi ma'aikatan sufuri a faɗin jihar Osun da su gujewa duk wani abu da zai kawo tada zauen tsaye.
Asali: Legit.ng