Home Back

Gwamna Ya Dakatar da Babban Hadiminsa, Ya Umarci Ya Bar Ofis Nan Take

legit.ng 2024/10/5
  • Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya dakatar da babban mataimakinsa na musamman kan harkokin jama'a, Emmanuel Adebisi ranar Laraba
  • Ya umarci dakatar da hadimin nan take har sai an yi bincike karkashin jagorancin shugaban ma’'aikatan fadar gwamnatin Osun, Kazeem Akinleye
  • Adeleke ya kuma umurci Kwamishinan Sufuri da ya taimaka wajen gudanar da taron sulhu a tsakanin bangarori masu adawa da juna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osogbo, jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke ya dakatar da Emmanuel Adebisi, babban mai taimaka masa na musamman kan harkokun kungiyoyin fararen hula.

Mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 3, ga watan Yuli, 2024.

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun.
Gwamna Ademola Adeleke ya dakatar da hadimi 1 a jihar Osun Hoto: @Osun_State_Gov Asali: Twitter

Gwamna Adeleke ya bayar da umarnin dakatar da hadimin nan tkae babu ba ta lokaci, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai gwamnan bai bayyana asalin dailin da ya jawo ya ɗauki matakin dakatarwa kan Mista Emmanuel Adebisi ba.

Sanarwar ta ce:

"Gwamna Adeleke ya dakatar da Emmanuel Adebisi nan take har sai na gama binciken da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jiha, Kazeem Akinleye zai jagoranta."

Bayan haka gwamnan ya gargaɗi ma'aikatan sufuri a faɗin jihar Osun da su gujewa duk wani abu da zai kawo tada zauen tsaye.

Asali: Legit.ng

People are also reading