Home Back

Cikin Shekara 1, An Kashe Ƴan Ta’adda 9,303, Kusan 10,000 Sun Miƙa Wuya

leadership.ng 2024/11/4
Cikin Shekara 1, An Kashe Ƴan Ta’adda 9,303, Kusan 10,000 Sun Miƙa Wuya

An samu gagarumar nasara a yaƙi da ta’addanci da ayyukan masu tada ƙayar baya a cewar daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba.

Nasarar Sojoji

Ya ce ƴan ta’adda 9,303 ne aka kashe, sannan mayakan Boko Haram da ISWAP 9,562 tare da iyalansu suka miƙa wuya. Bugu da ƙari, jami’an tsaro sun kuɓutar da mutane har 4,641 da aka yi garkuwa da su tare da kame ƴan ta’adda 6,998.

Nasarar Ƴansanda

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta bayar da rahoton zarge-zarge 16,200 daga cikin 29,052 da ake tuhuma da laifukan da suka hada da kama su da laifin fashi da makami da garkuwa da mutane da kuma fyade.

Rundunar ta kuma ceto mutane 1,713 da aka yi garkuwa da su, tare da kwato motoci 1,465 da babura, da bindigogi 2,566, da harsasai 19,310.

Nasarar NSCDC

A halin da ake ciki kuma, hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya NSCDC, ta daƙile hare-hare har sau 48 a makarantu tare da tarwatsa wuraren hakar ma’adanai 1,975 ba bisa ƙa’ida ba. Sun kuma bankaɗo tare da lalata matatun mai guda 165 da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.

Nasarar Kwastam

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta taka muhimmiyar rawa, inda ta samar da sama da tiriliyan 3.99 a cikin kuɗaɗen shiga tare da kwace haramtattun makamai, da muggan kwayoyi.

Sun kwato alburusai masu yawa tare da daƙile ayyukan miyagun laifuka da suka shafi haramtattun harƙyallar man fetur, tare da kama lita 50,000 na haramtaccan man fetur.