Home Back

Arewa Maso Gabas: Janar Buratai Ya Bukaci Kawo Karshen Matsalar Tsaro Cikin Gaggawa

legit.ng 2024/6/30
  • Tsohon shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai ya yi magana kan tsaro a Arewa maso gabashin Najeriya
  • Tsohon shugaban sojojin ya bukaci magance matsalolin tsaron yankin kafin lamarin ya kai ga yadda za a gaza magance sa
  • Laftanal Janar Tukur Buratai ya yi jawabin ne a yayin wani taro da jami'ar Maiduguri ta shirya a jiya Litinin, 27 ga watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi kira kan magance matsalolin tsaro a Arewa maso gabas.

Buratai
Buratai ya bukaci a kawo karshen Boko Haram. Hoto: Tukur Buratai Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Laftanal Janar Buratai ya yi jawabin ne a yayin taron da tsangayar tarihi a jami'ar Maiduguri ta shirya.

A jiya Litinin ne jami'ar ta shirya taron inda Laftanal Janar Buratai mai ritaya ya kasance cikin manyan baki da aka gayyata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buratai: Ya kamata a gama da Boko Haram

A yayin da yake jawabi, Laftanal Janar Tukur Buratai ya yabi sojojin Najeriya bisa kokari da suke a yankin Arewa maso gabas.

Duk da haka ya ce ya kamata yakin da ake da tsageru ya kammala, kar ya dauki tsawon lokaci kamar yakin Colombia da Sri Lanka.

Kokarin da Janar Buratai ya yi lokacinsa

Har ila yau, Laftanal Janar Buratai ya bayyana irin kokarin da jami'an soji suka yi a yankin a lokacin da yake jagorantar su.

Ya bayyana cewa a karkashinsa sojoji sun kwato ƙananan hukumomi tara da yan Boko Haram suka kwace cikin wata biyar.

UNIMAID ta fuskanci barazanar Boko Haram

Shugaban jami'ar Maiduguri ta yi karin haske kan yadda jami'ar ta cigaba da karatu duk da yawaitar hare-haren yan bindiga.

Farfesa Aliyu Shugaba ya ce jami'ar ta yi halin maza ta cigaba da karatu duk da hare-haren yan kunar bakin wake guda hudu da aka kawo musu.

An ba Janar Buratai Sarauta a Biu

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Sarkin Biu, Dr Umar Mustapha II, ya bai wa tsohon shugaban hafsan soji, Tukur Buratai sarauta.

An nadawa Buratai sarautar Betaran Biu a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoban 2023, saboda gudunmawar da ya bai wa masarautar ta Biu.

Asali: Legit.ng

People are also reading