Home Back

Sake Shan Kaye Game Da Batun Yankin Taiwan A Wajen WHA Ya Nuna Cewa Yunkurin Ware Taiwan Daga Kasar Sin Ba Zai Yi Nasara Ba

leadership.ng 2024/7/5
Sake Shan Kaye Game Da Batun Yankin Taiwan A Wajen WHA Ya Nuna Cewa Yunkurin Ware Taiwan Daga Kasar Sin Ba Zai Yi Nasara Ba

A wajen babban taron hukumar kiwon lafiya ta duniya karo na 77 ko kuma WHA a takaice da aka yi jiya Litinin 27 ga wata, an ki yarda da shigar da daftarin shirin da wasu kasashe ‘yan kalilan suka bullo da shi, cikin ajandar taron, wato gayyatar yankin Taiwan ya halarci taron a matsayin ‘yar kallo. Ke nan, a jerin shekaru 8, WHA ya ki amincewa da shigar da hukumar Taiwan cikinsa, al’amarin da ya nuna cewa, manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, babban fata ne na baki dayan al’umma.

Kasar Amurka da yankin Taiwan sun hada baki don saka batun siyasa a cikin WHA, al’amarin da kasa da kasa suka fahimta sosai, tare kuma da maida martani yadda ya kamata. A ‘yan kwanakin nan, akasarin kasashen duniya sun jaddada wa kasar Sin matsayinsu na tsayawa kan kudiri mai lamba 2758 da aka zartas a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, tare kuma da nuna cikakken goyon-bayansu ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kin yarda da shigar da yankin Taiwan cikin WHA, kuma kasashe sama da dari sun goyi bayan matsayin kasar Sin ta hanyar gabatar da sako na musamman zuwa ga babban darektan hukumar kiwon lafiya ta duniya.

Kasar Sin daya ce tak a duniya, kana, Taiwan wani yanki ne na kasar. Duk wani yunkurin da mahukuntan jam’iyyar Democratic Progressive da kasashe ‘yan kalilan suka yi, ba zai sauya hakikanin gaskiya ba. Wato manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, ba za ta sauyu ba, sa’annan yunkurin balle Taiwan daga kasar Sin bisa dogaro da sauran kasashe, da yunkurin kawo tsaiko ga ci gaban kasar Sin bisa hujjar batun yankin Taiwan, duk zai ci tura. (Murtala Zhang)

People are also reading