Home Back

Ramadan: Abba Kabir Ya Yi Zazzafan Gargadi Kan Rabon Kayan Tallafi Karo Na 4 a Kano

legit.ng 2024/5/11
  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shirya sake rabon kayan tallafi a watan Ramadan a karo na hudu a jihar
  • Gwamna Abba Kabir ya yi gargadi mai tsauri kan masu karkatar da kayan inda ya ce ba za su ji da dadi ba
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da rabon shinkafa buhu 112,220 domin tallafawa marasa karfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya tura sakon gargadi ga masu son kawo cikas a rabon kayan tallafi a jihar.

Abba Kabir ya yi wannan gargadin ne yayin kaddamar da rabon kayan tallafin karo na hudu a Kano.

Abba Kabir ya sake kaddamar da rabon kayan tallafi a karo na 4, ya yi gargadi
Abba Kabir ya gargadi masu karkatar da kayan tallafi da su guji fushin hukuma a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf. Asali: Facebook

Wane mataki Abba Kabir zai dauka?

Gwamnan ya ce zai dauki mummunan mataki kan wadanda ke shirin karkatar da kayan don biyan bukatar kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci yin adalci a rabon kayan domin tabbatar da ya isa wurin wadanda aka yi dominsu a jihar, a cewar Daily Trust.

An kaddamar da rabon kayan ne domin zagaye dukkan ƙananan hukumomi 44 da ke fadin jihar baki daya.

Yawan abinci da za a raba a Kano

Gwamnan Kano ya sanar da rabon buhunan shinkafa 112,220 masu nauyin kilo 25 ga gidaje musamman na marasa hali a jihar.

Abba Kabir ya ce za a fara rabon kayan ne daga yankin Kano ta Kudu kafin ci gaba da rarraba kayan ga sauran yankunan jihar.

Ana sa ran wannan tallafi sai taimakawa akalla gidaje 224,440 a jihar musamman ga mabukata domin samun sauƙi a watan Ramadan.

Kafin fara rabon kayan, gwamnan ya zagaya domin ganewa idonsa yanayin kyawun shinkafar da za a raba, cewar rahoton Leadership.

Abba ya haramta fina-finan 'yan daba

Mun kawo muku labarin cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya ba da sabon umarni ga masu shirya fina-finai a masana'antar Kannywood.

Gwamna ya dakatar da su daga shirya fina-finai da ke ɗauke da 'yan daudu da kuma 'yan daba a jihar.

Wannan bai rasa nasaba da yawan lalacewar tarbiyya da ake samu a jihar musamman na 'yan daba a kwanaki nan.

Asali: Legit.ng

People are also reading