Home Back

Kwara: An Cafke Likita da Wasu 4 da Zargin Satar Mahaifa da Cibiyar Jariri, Sun Fadi Gaskiya

legit.ng 2024/6/26
  • Dubun wasu ma'aikatan jinya ta cika yayin da aka cafke su da zargin batar da mahaifa da kuma cibiya bayan haihuwar jariri
  • Rundunar 'yan sanda a jihar Kwara ta yi nasarar cafke likita da kuma masu taimaka masa guda hudu kan zargin
  • Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, Ejire-Adeyemi Toun ta tabbatar da haka inda ya ce an kaddamar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Rundunar 'yan sanda a jihar Kwara ta cafke wasu jami'an lafiya biyar kan batar mahaifa da cibiya bayan haihuwar jariri.

Lamarin ya faru ne a asibiti Iloffa da ke karamar hukumar Oke-Ero da ke jihar a karshen makon da ya gabata.

An kama wani likita kan zargin satar cibiyar jariri
Yan sanda sun cafke likita a Kwara kan zargin satar mahaifa. Hoto: Nigeria Police Force. Asali: Twitter

An dakile shirin kona asibiti a Kwara

Wadanda ake zargin da ke amsa tambayoyi sun hada Dakta Ajibola da ma'aikatan jinya Rukayat Adeloye da Aishat Awolusi da Peace Alabi da Toyin Adewunmi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa sai da dattawan yankin Odo-Owa suka saka baki kafin aka dakile matasa wurin cinnawa asibitin wuta.

Mahaifiyar jaririn, C. B Williams ta ce ta yi korafi ne bayan likitoci sun gagara gabatar da mahaifa da kuma cibiya bayan haihuwar jaririn.

Williams wacce malamar makaranta ce ta ce wasu daga cikinsu suna ba ta hakuri yayin daya ta ce ta jefar a cikin rami.

Ma'aikatan jinyar daga bisani suka ce an jefar da mahaifar amma suna tsammanin kare ya cinye, cewar rahoton Vanguard

"Ta yaya za a ce cibiya da mahaifa na sabon jariri da aka haifa ya bace, duk mun san illar haka."
"Wasu ma'aikatan suna cewa na yi hakuri an yi kuskure sai wacce ta karbi haihuwar ke cewa ta jefa a rami amma ba su gani ba watakila kare ya cinye."
"Ina neman rundunar 'yan sanda ta yi kwakkwaran bincike domin gano gaskiyar lamarin tare da adalci."

- C. B Williams

Ƴan sanda sun yi magana kan lamarin

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Ejire-Adeyemi Toun ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma'a 17 ga watan Mayu.

Toun ta ce rundunarsu ta kaddamar da binciken sirri domin gano gaskiyar lamarin tare da ɗaukar mataki.

An rufe wata kasuwa a Kwara

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Kwara ta rufe mayankar abbatuwa da ke kasuwar Mandate na wucin gadi bisa zargin samun guba a naman dabbobi.

Babban sakataren ma’aikatar Muhalli, Dakta Abubakar Ayinla ya ce gwamnati ta dauki matakin rufewar ne domin ta samu damar yin feshin magani a kasuwar.

Asali: Legit.ng

People are also reading